An yi wata karamar dirama a kwaryar Majalisar Dattawa a ranar Talata yayin da shugaban marasa rinjaye na majalisar Sanata Enynnaya Abaribe (Mai wakiltar mazabar Abia ta Kudu) ya gaza cimma burinsa na sauya sheka zuwa jam’iyyar APGA bisa wasu dalilai.
Lamarin dai ya faru sakamakon manta wa da wasikar sauya sheka da shugaban Majalisar Sanata Ahmad Lawan ya yi a gida. Kafin a amince da batun sauya shekar dole ne sai an karanta takarar a gaban Majalisar.
- Lawan Na Fuskantar Barazanar Rasa Kujerarsa Wanda Ya Maye Gurbinsa Ya Ki Janye Masa
- Nasarar Tinubu A Takarar Shugaban Kasa: Na Dauki Mataki Na Gaba – Lawan
Wani labari makamancin wannan, kusoshi biyu na jam’iyyar APC, Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi da Adamu Aliero a hukumance sun koma jam’iyyar PDP.
An karanta wasikar canza jam’iyyar wadda Sanata Yahaya da Aliero suka aike a zaman majalisar na ranar Talata.
‘Yan Majalisar biyu masu wakiltar mazabar Kebbi ta Arewa da Kebbi ta tsakiya.
Sauya shekar kusoshin APC biyun ya kawo adadin Sanatacin PDP 39 a maimakon 38 a baya, idan aka cire Abaribe da ya kimtsa komawa APGA a ranar Laraba.
Hakan kuma ya rage yawan sanatocin APC daga 71 zuwa 69