Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya ta ya tsohon gwamnan jihar Legas kuma Jagoran APC na Kasa Ahmad Bola Tinubu murnar lashe zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa a inuwar jamiyyarsa, APC.
Lawan a cikin sanarwar da ya rattabawa hannu da kansa a yau Laraba ya ce, ya ji dadi ganin yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin ba tare da wani tayar da Jijiyar Wuya ba , inda ya yi nuni da cewa, samun nasarar zaben ta nuna karfin da APC take da shi wajen tafiyar da siyasar ta ta cikin gida ba tare da wata tangarda ba.
Da ɗimi-ɗiminsa: Wani Bene Mai Hawa Uku Ya Ruguzo A Kano
A cewarsa, zai yi aiki tukuru domin Jamiyyar APC ta kai ga nasara a zaben kakar shekarar 2023 inda ya cigaba da cewa, nasarar da Tinubu ya samu, ta nuna cewa, shi ne aka fi so.
Lawan ya ci gaba da cewa, bisa ga la’akari da irin kwarewar da Bola yake Da ita ta aikin gwamnti da kuma yadda ya saudaukar da lokacinsa wajen gina APC da kuma kwarin gwiwar da yake Da shi wajen tabbatar da dorewar mulkin demokiradiyya a kasar nan hakan ne ya sa ‘ya’yan APC suka aminta da Bola.
A karshe Lawan ya ce, “Bana wata tantama, kwarewar da Bola yake da ita za ta taimaka wa jamiyyar mu ta shiga zaben 2023 da kwarin gwiwa domin ta samu nasara”.