Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin da kasashen kungiyar hadin gwiwar yankin Gulf (GCC) a takaice, abokan huldar juna ne na zahiri.
A jawabin da ya gabatar a yayin taron shugabannin Sin da GCC da aka gudanar Jumma’ar nan, Xi ya yi kira ga sassan biyu, da su kasance abokan hadin gwiwa wajen inganta hadin kai, da ci gaba da tsaro da wayewar kai.
Bugu da kari, shugaba Xi ya gabatar da shawarwari kan manyan fannoni guda biyar na hadin gwiwa a cikin shekaru uku zuwa biyar dake tafe, wadanda suka hada da makamashi da harkokin kudi, da zuba jari, da kirkire-kirkire da sabbin fasahohi da harkar sararin samaniya, da harshe da kuma al’adu. (Ibrahim)