ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hukumar NPA Na Son Tara Kuɗaɗen Shiga Naira Tiriliyan 1.2 A 2025

by Bello Hamza
1 year ago
NPA

Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta bayyana cewa, ta yi hasashen Tarawa Gwamnatin Tarayya kudaden shiga Naira tiriliyan 1.28, a shekarar 2025.

Shugaban Hukumar ta NPA Abubakar Dantsoho, ya sanar da haka a ranar Litinin a babban birnin tarayar Abuja.

  • Hukumar NPA Ta Bayar Da Kwangilar Aikin Ruwa Na Tashar Lekki
  • Shugaban NPA Ya Sha Yabo Kan Yadda Ya Bunƙasa Tashar Jiragen Ruwa Ta Onne

Dantsoho, ya sanar da haka ne, a lokacin da ya bayyana a zaman da Kwamitin Majalisar wakilai da ke lura da al’amuran harkokin Jiragen Ruwa.

ADVERTISEMENT

A cewar Dantsoho, kaso 40 a cikin dari na kudaden shigar da ake son Tarawa, za su haura Naira biliyan 894.8, da Hukumar ta yi, hasashen tarawa, a shekarar 2024.

Shugaban ya kara da cewa, Hukumar ta NPA ta yi kasafin sama da wannan adacin, wanda kuma take son tarawa, musamman domin ta kara inganta ayyukanta, wadanda kuma za yi dai, dai da yadda ake gudanawar a fadin duniya.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

Ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA, ta yi kasafin da dara haka, na wannan adadin, musaman ganin cewa, ta na burin, kara inganta ayyukanta, yadda za su yi dai-dai, da yadda ake gudanar da ayyukan, a sauran Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya.

Shugaban Hukumar ya kuma sanar da cewa, a shekarar 2024, Hukumar ta NPA, kudin shigar da ta yi hasashen Tarawa daga na Naira biliyan 865.39, sun karu zuwa Naira biliyan 894.86.

“ Wannan ya nuna yadda Hukumar ta NPA, ta mayar da hankali da kuma kara zage Damtse wajen ganin ta Tarawa Gwamnatin Tarayya kudaden shiga, masu yawa,”  A cewar Dantsoho.

Shugaban ya kuma bayyana cewa, kudaden shigar da Hukumar ke hasashen Tarawa a shekarar ta 2025, za ta samar da su ne, daga harajin da take karba daga gun Jiregen Ruwan da aka yo jigar kaya wanda ya kai Naira biliyan 544.06 da Naira biliyan  413.06 na Jiragen Ruwa da kuma wasu sauran kudade na Naira biliyan 249.69 sai kuma kudaden shiga, na sasehn gudnar da mulki, da suka kai Naira biliyan  73.07.

Shi kuwa a na sa jawabin, a zaman na Kwamitin, Shugaban Kwamitin Nnolim Nnaji, ya yi kira ga Hukumar ta NPA, da ta kara kaimi kan nasarorin da ta samar, tare da kuma kara inganta kayan da take gudanar da ayyukanta, musaman ta kuma bayar da gagarumar gudunmawa, wajen kara samar da hanyoyin  ayyukan yi, ga ‘yan kasar nan.

Nnaji ya sanar da cewa, Hukumar ta NPA, ta kasance wata ginshike ce, wajen bayar da gagarumar gudunmawa na kara bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

Shugaban ya kuma bukaci Hukumar da kara mayar da hankali, kan burukan da take son cimma duka manyan kalubalen da take fuskanta.

“Babu kata kasa a fadin duniya da za ta iya samar da wani ci gaba mai dorewa, ba tare da yin aiki, da sanarorin da Hukumar Jiragen Ruwa, ke samarwa ba,” Inji Shugaban.

Ya ci gaba da

“Hukumomin Jiragen Ruwa na kowacce kasa a fadin duniya, sune kashin bayan ci gaban tattalin arzikin kasa, musamman kan yadda ake gudanar da hada-hadar fitar da kaya da kuma shigar da su,” A cewar Nnaji.

Kazalika, Shugaban Kwamitin ya sanar da cewa, namijin kokarin da Hukumar ta NPA take kan yi, abin yabawa ne, kuma hakan, zai kara taimaka wa, wajen kara samar da ayyukan yi, a kasar nan.

“Hukumar ta NPA, ba wai kawai tana aikin tara kudaden shiga ba ne, ta kasance wata babbar kadara ce, wajen samar da ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya da kuma kara habaka, tattalin arzikin kasar,” Inji Shugaban.

Nnaji ya bayyana cewa, wannan Kwamtin na jiran ya ga dabarun da Hukumar za ta yi amfani da su, musamman domin kara bunkasa kudaden shigar da kuma kara samar da damar ayyukan yi, ga ‘yan kasar nan, ta hanyar kasafin kudinta, na shekarar  2025.

NPA
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

MASU ALAKA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas
Tattalin Arziki

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

September 4, 2026
NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
Tattalin Arziki

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

September 4, 2026
NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja
Tattalin Arziki

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

August 28, 2026
Next Post
Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa

Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.