Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya ce, sun gabatar da sabbin dabaru, da manufofi da tsare-tsare da nufin kyautata rayuwar al’umar jihar a cikin shekaru ukun da suka gabata, yana mai cewa, sun dage don sadaukar da kai wajen cika alkawurran yakin neman zaben da suka yi.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yaba da daurarriyar demokradiyya da aka samu tsawon shekaru 23 ba tare da katsewa ba a Nijeriya, lamarin da ya bayyana cewa shi ne irin sa mafi tsawo a tarihin mulkin farar fula tun bayan samun ‘yancin kai.
- ‘Kwankwaso Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023’ —Jideogu Ogbu
- Lalacewar Babbar Hanyar Lantarki Ta Kasa Na Tabbatar Da Gazawar Nijeriya A Komai – Atiku
Inuwa ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da sabuwar makarantar firamare da karamar sakandare ta Alabura a Anguwar Ƙumbiya-Ƙumbiya da ke fadar jihar, yake cewa, “A bayyane yake cewa demokradiyyar Nijeriya ta kafu, duk da dimbin kalubalen da kasar ke fuskanta. Muna iya fahimta da sasanta kan mu ba tare da daukar makamai ba”.
“Hakan yana kara nuna bunkasar mu a siyasance da tsayin dakan mu duk da bambancin mu na yanki da kabila da addini. Ko shakka babu dawowa mulkin dimokuradiyya a 1999 ya kawo kusanci ga al’umma ta yadda za a magance bukatu da buri na kungiyoyi daban-daban a kasar nan”.
Ya ce a Jihar Gombe, babu shakka cewa dimokuradiyya ta kawowa jihar ci gaba mai dorewa, “Ya zuwa yanzu gwamnatocin farar hula uku suka yi mulki inda mu daga bisani muka biyo baya har yanzu muke cika shekaru uku, mun yi bakin kokarinmu wajen ganin mun kara tabbatar da nasarorin da gwamnatocin da suka gabata suka samu tare da gyara kura-kuran da muka tarar.
“Rahoton bibiyar al’amaura na shekaru ukun da suka gabata ya nuna cewa mun samu kaso 90 cikin dari na nasarori wajen cika alkawuran da muka yiwa al’ummar jihar nan, hakika babban aiki ne wannan, tun da muka iya cika alkawuran da muka yi wa al’ummarmu a wannan lokaci na tabarbarewar tattalin arzikin duniya da rashin tabbas, amma idan muka yi la’akari da jajircewar mu, da aiki tukuru da juriya, da kuma kokarin sarrafa ‘yan kudaden da muke dasu, mun samu damar aiwatar da ayyuka da suka rataya a wuyan mu, wadda hatta abokan adawar siyasar mu sun mika wuya”.
Gwamnan ya ce yayin da gwamnatinsa ke cika shekaru uku a kan karagar mulki, zai ci gaba da maida hankali tare da himmatuwa wajen inganta rayuwar al’umma ta hanyar samar da ababen more rayuwa na kyautata zamantakewar al’umma cikin adalci, da tabbatar da zaman lafiya da tsaro, da doka da oda tare da samar da damammaki ga al’ummar jihar.
Ya bayyana tabbacin cewa ta hanyar samar da tsarin dimokuradiyya ne kawai jihar za ta iya ci gaba da biyan bukatun jama’a tare da tabbatar da amincewar su ga gwamnatin jihar karkashin jagorancin sa. Gwamna Inuwa Yahaya ya yi amfani da damar wajen yaba wa hangen nesa, da jajircewa da kishin kasa na gundumar Kumbiya Kumbiya da suka sadaukar da gidajensu da muhallinsu don bai wa Gwamnati damar kafa makarantar tare da basu tabbacin gwamnati na ci gaba da nuna goyon baya da taimako a gare su.