Wasu ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Gombe biyu sun fice daga jam’iyyar APC sun shiga jam’iyyar adawa ta NNPP.
‘Yan majalisun sun hada da Hon. Hamza Adamu da ke wakiltar mazabar Balanga ta kudu da kuma Hon. Bappah Usman Jurara mai wakiltar mazabar Funakaye ta kudu a Majalisar Dokokin Jihar.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Sun Kone Gidaje 22 A GombeÂ
- Matafiya 17 Da Suka Taso Daga Legas Zuwa Gombe Sun Kone Kurmus A Hadarin Mota
Wakilinmu ya labarto mana cewa ‘Yan Majalisar sun koma NNPP bayan wata ganawa da suka yi da dan takarar Gwamnan jam’iyyar a jihar, Alhaji Khamisu Ahmed Mailantarki.
Ficewar ta su na zuwa ne kwana guda bayan da jam’iyyar APC ta kaddamar da gangamin yakin neman zaben gwamnan Bihar na 2023.
‘Yan majalisun sun ce, sun dauki wannan matakin ne saboda kishin jihar da kuma al’umarsu. Sun Zargi Dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC da gazawa wajen iya mulki da kasawa wajen hada kan al’umar jihar.