Kimanin matafiya 17 da suka taso daga jihar Legas zuwa jihar Gombe a cikin mota kirar Toyota Hiace mai cin fasinjoji 18 tayi taho mu gama da tirelar Daf, inda matafiyan suka kone kurmus.
Toyotar mai dauke da lamba GME 20 XA, inda kuma Daf din ke dauke da lamba BAU 632 XA, sun karon ne akan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Lamarin wanda ya auku a yau talata, matafiya hudu da suka ta so daga jihar Gombe ne kadai suka tsira da ransu, inda summa, sun samu munanan raunuka, inda jami’an FRSC suka mika su zuwa ga babban asibitin da ke a yankin Abaji don a duba lafiyar su.
Wani ganau Kabiru Garba ya ce, hadarin ya auku ne a mahadar ababen hawa ta Yaba daura da babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Ya ce, Toyotar ta ta so ne daga Abuja zuwa Gwagwalada a guje, inda ta bigi Sad din.
Kwamandan hukumar FRSC na shiyyar mista Samuel Ogar Ochi, ya tabbatar da aukuwar hadarin, inda ya danganta hakan akan mugun gudu direban na Toyotar.