Babban Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Isah Jere Idris, ya ba da umarnin gaggauta kafa reshen hukumar a dukkan filayen jiragen sama na kasa da kasa da ke kasashen waje domin a samu tsarin samar da fasfo ga duk ‘yan Nijeriya da ke zuwa gida a wannan lokaci.
Shugaban hukumar ya bayyana haka a wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Litinin a Abuja, ta hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Anthony Akuneme.
- NIS Ta Ƙara Ƙaimin Aiki, Inda Shugabanta Ya Buɗe Sabon Ofishin Ingancin AikiAiki
- Shugaban NIS Isah Jere Ya Sanar Da Karin Girma Ga Jami’ai 4,526
Shugaban ya ce hukumar ta kuma umarci ofisoshin fasfo a fadin kasa da su baiwa irin wadannan ‘yan kasar da ke zaune a wajen kasar muhimmanci da kuma iyalansu la’akari da cewa yawancinsu suna da iyakantaccen lokacin komawa ƙasashensu.
“CGIS ta tabbatar da aniyar hukumar na ci gaba da bayar da ingantaccen tsarin aiki ga duk ‘yan Nijeriya a gida da waje, da kuma wadanda ba ‘yan Nijeriya ba da ke da bukatar kowane taimako daga hukumar.”
Tsarin fasfo mai sauri na wannan lokacin Kirisimeti ya fara ne makonni kadan da suka gabata tare da bude ofisoshin fasfo a ranar Asabar din nan, kuma zai ci gaba har zuwa 31 ga Janairu 2023.