Akalla mutane 55 ne suka mutu a ranar Talata, yayin da ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru da dama ta barke a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi.
Manyan tituna da ke tsakiyar birnin Kinshasa, mai kimanin mutane miliyan 15, ruwa ya shafe su sa’o’i da dama.
- Kasan Wadanda Suka Kawo Boko Haram, Martanin Gwamnatin Tarayya Ga Atiku
- Kasar Sin Ta Gudanar Da Bikin Tunawa Da Wadanda Aka Halaka A Birnin Nanjing
Shugaban ‘yansandan birnin, Janar Sylvano Kasongo, a wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dilancin labarai na AFP, ya bayar da rahoton cewa akalla mutane 55 ne suka mutu.
Haka zalika, zabtarewar kasa ta afku a gundumar Mont-Ngafula da ke kan tudu, inda ta lullube wata babbar hanyar samar da kayayyaki da ta hada babban birnin kasar da Matadi, yankin da ke dauke da tashar jiragen ruwa da ta taso daga kogin Kongo zuwa mashigar ruwa ta Tekun Atlantika.
Firaministan kasar, Jean-Michel Sama Lukonde ya shaida wa manema labarai cewa mutane kusan 20 ne suka mutu a wurin da zabtarewar kasar ta auku.
Ya ce ana ci gaba da neman wadanda baraguzan gine-gine suka rufe.
Ya kamata a sake bude babbar hanya ga kananan ababen hawa, amma za a iya daukar “kwana uku ko hudu” kafin a bude wa manyan motoci, in ji Firaministan.