• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Maka El-Rufai Da Wasu 13 A Kotu Kan Nada Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli

by Abubakar Abba
3 years ago
El-Rufai

Tsohon Wazirin masarautar Zazzau, Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu, ya maka Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, masarautar Zazzau da kuma wasu mutane 12 a gaban babbar kotun jihar.

Aminu, ya maka su ne a gaban kotun a kan nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19.

  • Da Dumi-Dumi: Jakadan Nijeriya A Sifaniya, Demola Seriki Ya Rasu
  • Karancin Mai: IPMAN Ta Yi Barazana Rufe Gidajen Mai Saboda Gargadin DSS 

Aminu, wanda na daya daga cikin masu nada sarki a masarautar Zazzau, ya bukaci kotun ta soke martaba Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau.

Da aka gabatar da kakar a jiya Laraba wasu daga cikin wadanda Aminu ya maka a gaban kotun akwai sarkin da marigayi Limamin Kona, Malam Sani Aliyu, wand a ya rasu a watan Yulin 2022.

El-Rufai ne dai nada Bamalli a matsayin sabon sarkin ne a ranar 7 ga watan Okutobar 2020, wanda a baya ya kasance jakadan Nijeriya ne a kasar Thailand.

LABARAI MASU NASABA

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a

A lokacin da aka gabatar da karar a jiya, alkalin kotun mai shari’a Isah Aliyu, ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Fabirairun 2023 don a bai wa lauyan wanda ake kakar damar yin nazari a kan karar tare da kuma gabatar wa da kotun hujjarsa a kan karar.

A tattaunawarsa da manema labarai jim kadan bayan zaman kotun, lauyan da ke tsayawa mai karar Barista Rabiu Saidu, ya ce, wanda yake tsayawa ya shigar da kakar ne saboda sauran wadanda suka kasance masu nada sarki, ba a ba su damar zabo wanda zai zama sarkin ba, inda hakan ya sabawa ala’adar nasarautar.

Ya kara da cewa, a bisa ka’ida masu zabo wanda zai zama sarkin, na tura wa gwamna sunayen wadanda za a nada a matsayin sarkin masarautar, inda ya ce, wanda a yanzu yake a kan karagar masarautar, sunansa baya a cikin sunayen da aka turawa gwamnan, saboda haka bai dace a nada shi sarkin ba, domin nadinsa, ya saba wa shawarar da masu zabo sarkin suka bayar.

Lauya mai tsaya wa masarautar Zazzau, Barista Aminu Usman Bamalli, ya ce, lauyan mai karar ya kamata ya gabatar da adireshin da zai kasance shi mazaunin ne a Kaduna kamar yadda doka ta 4 da ta 6 a tsarin aikin kotun jihar ta tanadar, inda ya ce, amma lauyan, ya kasance mazaunin Abuja ne kuma hakan zai yi matukar wahala a gare su wajen gabatar masa da takardunsu a kan lokaci.

Kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 23 ga watan Fabirairun 2023.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara
Manyan Labarai

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a
Manyan Labarai

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a

October 20, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas
Manyan Labarai

‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta

October 20, 2025
Next Post
Jirgin Kasa Ya Yi Awon Gaba Da Mota Dauke Da Fasinjoji A Abuja

Jirgin Kasa Ya Yi Awon Gaba Da Mota Dauke Da Fasinjoji A Abuja

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

October 20, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025
Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

October 20, 2025
Alkaluman GDP Na Sin Sun Fadada Zuwa Kaso 5.2 A Watanni 9 Na Farkon Bana

Alkaluman GDP Na Sin Sun Fadada Zuwa Kaso 5.2 A Watanni 9 Na Farkon Bana

October 20, 2025
Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta

Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta

October 20, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 20, 2025
Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.