Jakadan Nijeriya a kasar Sifaniya, Demola Razaq Seriki, ya rasu yana da shekara 63 a duniya.
Marigayin an haifesa ne a ranar 30 ga watan Nuwamba, 1959, ya kasance jigo ne a jam’iyyar APC a Jihar Legas kuma ya taba zama ministan tsaron Nijeriya.
- Yawan Tsofaffi Masu Sama Da Shekaru 60 A Sin Da Suka Karbi Alluran Rigakafin COVID-19 Ya Zarce Miliyan 240
- Majalisar Dattawa Ta Bukaci CBN Ya Sake Nazarin Dokar Takaita Cirar Kudi
Sanarwar mutuwar tasa ta fito ne daga wajen dansa a ranar Alhamis.
Talla
Sanarwar mutuwar ta ce marigayin ya mutu ne a garin Madrid da ke kasar Sifaniya da safiyar ranar Alhamis.
Talla