Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta bayyana cewa, za a iya kawo karshen cin zarafin da ake yi wa mata da kananan yara a sassan kasar nan duk kuwa da yadda ake samun karuwar lamarin a ‘yan shekarun nan.
Aisha Buhari ta sanar da haka ne taron kungiyar matan gwamnonin Nijeriya karo na 3 a garin Abuja kwanakin baya, taron mai taken, “Fadakar da al’umma a kan dokar ta-baci a kan cin zarafin mata’.
Ta kuma bukkaci kungiyar ta tabbatar da dorewar gangamin musamman ganin a halin yanzu an samu nasarar zartar da dokar kariya ga mata da kananan yara a jihohi 34 na tarrayar Nijeriya.
Uwargidan Shugaban kasar wadda ta samu wakilcin mataimakiyarta ta musamman a kan harkokin mata, Rukayyatu Abdulkareem Gurin, ta kara da cewa, lamarin cinzarafin mata na daya daga cikin abubuwan da aka tattauna a taron kwanaki 16 da aka yi inda waklilai daga kasashen duniya suka samu halarta, musamman ganin mastala ce da ake fama da ita a sassan duniya.
Ta yaba wa matan gwamnonin a kan yadda suka hada kai don ganin an samar da yanayi na kare mata da kananan yara daga cutarwa ta kowacce fuska.
Ta ce, “Hanyar samar da daidato da hanyoyin samun aiki ga mata na da matukar muhimmanci, Nijeriya ta yi gaggarumar nasara a wannan fannin, musamman in aka lura da yadda aka zartar da dokar haramta cin zarafin mata ‘ Biolence Against Persons Prohibition (BAPP)’ a wasu jihohi 34 na tarrayar kasar nan.
Ta kuma kara da cewa, kungiyar matan gwamnonin sun kudurin aniyar aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki doin ganin an rage yadda ake cin zarafin mata da kananan yara a kasar nan.
“Yakamata mu kuduri aniyar tabbatar da ganin kowacce mace ko yarinya ta samu ‘yancin rayuwa tare da cikakken kariya daga dukkan abin da zai iya cutar da ita,” in ji ta.
Ana shi jawabin, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya, kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya tabbatar wa da mata cewa, gwamnoni za su cigaba da bayar da gudummawar da ta kamata don ganin an kawo karshen cin zarafin mata a Nijeriya.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa, saura jihohi 2 da basu sanya hannu a kan dokar kariya ga mata ba za su sa hannu nan ba da dadewa ba, ya kuma yaba wa matan gwamnonin a kan wannan kokarin, da yaba masu a kan yadda suka samar da yanayin shirin zai cigaba koda a bayansu ne.
Tunda farko, shugabar kungiyar na matan gwamnonin Nijeriya kuma uwargidan Gwamnan Jihar Sakkwato, Hajiya Mariya Aminu Tambuwal, ta ce, cikin makasudin kafa kungiyar sun hada da tattara masu ruwa da tsaki don ganin an fuskanci matsalar cin zarafin mata a Nijeriya.
Ita a nata jawabin, Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen, ta yaba wa Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a kan dokoki masu tsauri ga masu cin zarafin mata a jihar, a dokar wanda aka sanya wa hannu a watan Satumba 2021, an tanadi yin dandake ga wadanda aka samu da cin zarafin mata.
Dokar da aka yi wa kwaskwarima ta tanadi duk wani magidanci da aka kama ya yi wa yarinya ko yaro da shekarunsa suke kasa da 14 fyade a yi masa dandaka yayin da macen da aka kama ta yi wa ‘yan yara fyade ita ma za a cire mata mahaifa.