Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ta yi nasarar cafke gurbatattun kwayoyi na Tiramadol da wasu nau’ikan na daban na sama da kudi miliyan 1.7 da aka boyesu cikin kwalayen taliyar yara da wasu kwalayen na daban.
An kunshe kwayoyin cikin kwalayen Taliyar yaran da nufin karkatar da hankula a filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa na Murtala Muhammed da ke Legas da kuma na jihar Gombe.
- NDLEA Ta Cafke ‘Yar Shekara 60 Da Mace Mai Juna-biyu Cikin Masu Harkallar Sayar Da Kwaya
- NDLEA Ta Cafke Wanda Take Nema Ruwa A Jallo Kan Badakalar Miyagun Kwayoyi
A cikin kayan da aka kama sun hada da kwayar Tiramadol na sama da 600,000, an kawo su cikin kasar nan daga Karachi na kasar Pakistan a jiragen Ethiopian daban-daban guda biyu wanda jami’an SAHCO suka kama a filin Jirgin saman Legas a ranar Litinin 12 ga watan Disamba.
A ranar Talata 13 ga watan Disamba an kuma yin nasarar kama kwayoyi guda 5,960 na Rohypnol boye cikin fakitin taliyar yara da ake son kaiwa zuwa Johannesburg da ke Afirika ta Kudu wanda jami’an SAHCO Export Shed suka kama.
Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya ce, wata mata Olaleye Adeola ce aka kama dauke da kayan cikin fakitin Taliyar yaran.