Baya ga sassauta matakan yaki da annobar COVID-19, tare da la’akari da tsayin daka da karfin tattalin arzikinta, manazarta sun yi imanin cewa, tattalin arzikin kasar Sin, zai farfado a shekarar 2023, kuma zai ci gaba da zama abin dogaro kana muhimmin karfin tattalin arzikin duniya a shekarar 2023.
Lawrence Loh, darektan cibiyar tafiyar da harkokin mulki da ci gaba mai dorewa a kwalejin koyar da harkokin kasuwanci na jami’ar kasar Singapore, ya shaidawa babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG cewa, duk da yanayin tattalin arzikin duniya da illolin annobar, tattalin arzikin kasar Sin abin a yaba ne matuka a shekarar 2022.
A ranar Juma’a ne aka kammala babban taron shekara-shekara kan aikin raya tattalin arzikin kasar Sin a birnin Beijing, inda aka tsara ka’idojin raya tattalin arzikin kasar na shekara mai zuwa, da tsara muhimman batutuwan da suka shafi harkokin tattalin arziki na shekara mai zuwa, gami da fadada bukatun cikin gida, da hanzarta gina tsarin masana’antu na zamani, da karfafa hukumomin jin dadin jama’a da kamfanoni masu zaman kansu, da jawo karin jarin waje, da kuma hana aukuwar manyan hadurra na tattalin arziki da kudi.
A kwanakin baya, rahotanni daga bankuna da dama na duniya sun yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar Sin, zai samu kyakkyawan sakamako a shekarar 2023, inda Morgan Stanley da Societe Generale, manyan kamfanonin ayyukan hada-hadar kudi na kasa da kasa guda biyu, sun yi hasashen karuwar kashi biyar cikin dari a shekarar 2023.
A halin da ake ciki yanzu, kamfanonin kasashen duniya da dama, suna fadada ayyukansu da zuba jari a kasar Sin. Alkaluman hukuma sun nuna cewa, a cikin watanni 10 na farkon bana, jarin kai tsaye daga kasashen waje da aka zuba a babban yankin kasar Sin, ya karu da kashi 17.4 bisa dari bisa makamancin lokaci na bara, zuwa dalar Amurka biliyan 168.34.(Ibrahim)