Yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da sakon taya murnar gudanar da “bikin nuna al’adun Larabawa” karo na biyar.
Xi ya ce, kasar Sin da kasashen Larabawa suna da dadadden zumunci, inda suke kara hada kansu don musanyar al’adu. Ya kuma jaddada fatansa cewa, kasar Sin da kasashen Larabawa za su yi amfani da wannan dama, don aiwatar da nasarorin da aka samu a wajen taron kolin Sin da kasashen Larabawa karo na farko, da yaukaka zumuncin gargajiya, da fadada mu’amalar al’adu tsakaninsu, da kara sanya kuzari ga dangantakar bangarorin biyu bisa manyan tsare-tsare, da taimakawa ga raya al’ummomin Sin da kasashen Larabawa masu kyakkyawar makoma ta bai daya a sabon zamanin da muke ciki. (Murtala Zhang)