Rundunar sojin sama da na kasa na Operation Hadarin Daji sun samu gagarumar nasara bayan da suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda sama da 40 akan babura a kauyen Malele da ke karamar hukumar Dansadau a jihar Zamfara.
An kai harin ne a ranar Asabar din da ta gabata a wani harin hadin gwiwa mai nasara tsakanin rundunar sojojin sama (NAF) da na kasa na sojojin Nijeriya, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, a cewar mazauna yankin, an samu kuskuren kashe wasu daga cikin mazauna yankin yayin farmakar ‘yan bindigar dajin dake yankin.
Wata majiyar soji ta bayyana yadda hedikwatar tsaro ta rarraba jami’anta wajen kai hare-hare da jiragen sama kan ‘yan fashin da ke addabar jama’a daga sassa daban-daban na kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp