Darakta-janar na kwamitin yakin zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LPPCO), Dakta Doyin Okupe, ya ajiye mukaminsa na daraktan yakin zaben.
Okupe a wata babbar wasika mai dauke da kwanan wata 20 ga watan Disamban 2022 da ya aike da ita kai tsaye ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi, ya ce, ya dauki wannan matakin ne lura da cewa a kashin kansa yana neman hanyoyin samun adalci ta hanyar shari’a d kokarin wanke sunansa ta hanyar shari’a, sannan da cewar kada a dalilinshi a samu karkatar da hankali kan alkawarin da ya yi na yin aiki tukuru a matsayin daraktan yakin zabe ya samu tangarda.
Ya ce, idan aka nada wani sabon darakta yakin zaben hakan zai bada dama a ci gaba da tafiyar da harkokin yakin zaben ba tare da wani hujumi ko damuwa ba.
Jaridar LEADERSHIP ta labarto cewa a ranar Litinin ne watan babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta samu Dakta Doyin Okupe da laifin karbar sama da naira miliyan 200 daga hannun tsohon mai bai wa shugaban kasa shawarori kan harkar tsaro (NSA), Kanal Sambo Dasuki (Mai ritaya) kan hakan ne ta masa daurin shekara biyu a gidan yari
Wasikar da ya aike na cewa, “Idan za ku iya tunawa dai a jiya na muka bayani kan kokarin da nake yi wajen neman adalci da kokarin wanke sunana ta hanyar shari’a. Ba na son ya zama a sanadin ni kadai a samu karkatar da hankali daga yakin neman zabenka.
“Kan hakan na sauka daga mukamina da fatan nada sabon darakta Janar na yakin neman zaben zai cigaba da gudanar da harkokin ba tare da wani hujumi ba,” a cewar Akupe.
Ya sha alwashin cewa zai cigaba da kasancewa tare da Peter Obi har zuwa ga samun nasarar zaben 2023, ya ce zai cigaba da kasancewa a tare da shi dari bisa dari.
Sannan Okupe ya wallafa ya shafinsa na Tuwita cewa, ya ajiye mukaminsa amma zai cigaba da kasancewa da Peter Obi dari bisa dari har zuwa lokacin da Allah zai ba su nasara a zaben 2023.
Idan za ku iya tunawa dai ya ke yanke hukuncin a ranar Litinin, Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu, ya ce, Okupe wanda shi ne ake kara na farko a karar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta shigar kan karya dokar amfani da kudade ta hanyar zargin babakere da dukiyar kasa.
Ya samu wannan hukuncin ne kan zarge-zarge guda 34 ko zabin biyan tara na N500,000.
Sannan kotun ta kuma sake yanke masa hukuncin zaman shekara biyu a gidan yari kan tuhume-tuhume 35 zuwa 59 ko zabin biyan tara na N500,000.