Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na badi, Bola Tinubu ya ce abokan hamayyarsa a wasu jam’iyyu ba su da nagarta.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata a garin Kalaba na Jihar Kuros Riba, yayin wani taro da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.
- Babu Matakin Da Muka Dauka Kan Murabus Din Okupe – Kwamitin Yakin Zaben Peter Obi
- Dilolin Miyagun Kwayoyi Da Barayin Gwamnati Ne Ke Adawa Da Sabon Tsarin CBN – Kungiyar Dalibai
Ya ce yana da yakinin cewa jam’iyyar APC za ta lashe dukkan zabukan shekara mai zuwa, yayin da ya shaida wa dimbin jama’ar da ke ta murna cewa yana da duk abin da ya dace don ya ci zabe ya kuma mulki kasar nan.
“Ba su da nagarta; ba su da gogewa, ba su da tarihi, ba su da mutunci, don haka duk abin da suke yi sai cin zarafi da zagi. Damuwata ita ce ci gaban Nijeriya, kuma abin da zan yi ke nan a matsayina na shugaban kasa,” in ji shi.
Tinubu ya kara da cewa, “Laifinmu ne kasar nan cikin shekaru 60 da suka gabata ba mu samu ci gaba ba, amma ciyar da Nijeriya gaba abu ne da ya kamata a yi.”
Tinubu dai ya dage da yakin neman zabensa, inda yake bayar da yakinin cewar zai lashe zaben 2023 da ke tafe.