Rundunar ‘yansandan jihar Kogi a ranar Laraba ta ce, ta yi rashin jami’anta guda biyu a wani harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa tawagarsu da suke sintiri a kan hanyar Agbaja da ke Lokoja.Â
A wata sanarwar da Kakakin ‘yansandan jihar Sifiritadan William Ovie Aya, ya fitar tare da raba wa ‘yan jarida a Lokoja, ya shaida cewar, ‘yan bindigan sun fito daga cikin daji ne suka yi kwantan-bauna wa tawagar ‘yansandan a lokacin da suke kan sintiri.
Aya ya kara da cewa: “Mun yi rashin jami’anmu guda biyu a musayar wutar da aka yi da ‘yan daban yayin da suka arce lokacin da aka yi karin jami’an da suka kawo daukin gaggawa.
“Kwamishina ‘yansandan jihar Kogi, CP Akeem A. Yusuf, ya gaggauta tura jami’ai domin tabbatar da kamo wadanda suka aikata wannan danyen aikin.
“Ya kuma umarci mataimakin kwamishinan ‘yansandan na sashin bincike da ya kaddamar da fara bincike kan wannan lamarin da ya faru.
“Kwamishinan ya kuma roki jama’an yankin da su taimaka wa ‘yansandan da bayanan da suka dace domin tabbatar da an kamo wadannan ke da hannu a aikin don ganin an dakile aniyar ‘yan ta’adda da ta’addanci.”