A daren Laraba ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya kai wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ziyara a gidansa da ke Abuja inda suka yi ganawar sirri.
Wannan shine karon farko da Osinbajo ya ziyarci Tinubu tun bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa wanda Tinubu ya lashe ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.
Nan da nan bayan kammala zaben fidda gwani, Tinubu ya kai wa Osinbajo ziyarar ba-zata a gidan sa da ke cikin fadar shugaban kasa, inda ya kawar da rade-radin da ake yi na cewa alakarsu ta da gule bayan fafatawar neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Jita-jitar rashin jituwar ta ta sake kunno kai yayin da aka rasa ganin sunan mataimakin shugaban kasan a jerin sunayen jagororin kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima.
Sai dai fadar shugaban kasa ta yi karin haske kan cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bukaci Osinbajo da sakataren gwamnatin tarayya (SGF) Boss Mustapha da a ba su uzuri daga ayyukan yakin neman zabe domin su mayar da hankali kan harkokin mulki.