Fitacciyar Jaruma kuma me shirya fina-finai, Jarumar da ta shafe tsahon shekaru ashirin da daya 21 cikin Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, HAJIYA ZULAIHATU ABDULLAHI ALIYU BEBEJI Wadda aka fi sani da MAMAN HAIDER cikin shirin Dadin kowa.
Jarumar ta yi batutuwa masu yawan gaske dangane da irin matsalolin da wasu jaruman ke fuskanta cikin masana’antar, tare da wariyar launin fata da ake nunawa wasu. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki tare da sunan da aka fi saninki da shi.
Sunana Hajiya Zulaihatu Abdullahi Aliyu Bebeji, wadda aka fi sani da Maman Haider ko Hajiya Zulai Gaida, ko Hajiya Gaida, mutanen gari kuma suna kirana da Uwa ta Gari, an fi sanina kuma da Attajira sunan fim dina kenan Attajira.
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
An haife ni a Jihar Kano karamar hukumar Bebeji, na taso a unguwar Brigade wato Gawuna, a nan na yi ‘yan matanci. Na yi karatu dai-dai gwargwado har zuwa aure. A yanzu ina da yara guda hudu Maza biyu, Mata biyu.
Me ya ja hankalinki har kika tsunduma cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta kannywood, kuma wanne rawa kike takawa a cikin masana’antar?
Har kullum idan aka tambaye ni wannan tambayar, amsar dai ba ta wuce guda daya wato shi komai mukaddari ne, abin da Allah ya tsara a rayuwarsa sai ya yi, amma ni ba zan ce ko sha’awa ce ko wani abun ba, kawai dai Allah ya nufe ni da shiga harkar kuma gani ina yi. Sannan rawar da nake takawa a ciki masana’antar shi ne; ina fitowa a matsayin uwa, kuma tun lokacin dana fara fim a wannan matsayin nake fitowa.
Kamar fannin Shirya fim ko Bada umarni ko Daukar nauyi fa, shin kina yin daya daga ciki ko kuwa iya fitowa matsayin Jaruma kawai kike?
Haka ne, na shigo harkar fim ‘industry’ tun 2002, shekara kusan 20 kenan. Na dan fara sai na bari, na dawo 2011 kamar shekara 11 da ta wuce baya, toh daga wannan lokacin zuwa yanzu na shirya fina-finai nawa na kaina (Producing). A 2013 akwai fim dina ME GORO, wajen 2016 mun yi MAHAIFIYAR MU, DAN ZAMAN DAKI, ATTAJIRA, fim dina ne na kaina, yanzu kuma ina cikin wani ‘Producing’ na fim me suna JAWAHIR. Fim din JAWAHEER ni nake Furodusin dinsa, fim din Alhaji Sa’idu Gwanja ne. Ni kuma ni ce furodusa, falillahil Hamdu muna dan shisshiryawa, kuma muna fitowa a ciki.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance, musamman yadda wasu ke kukan samun shiga a yanzu?
Eh! toh gaskiya kamar yadda kika fada akwai gwagwarmaya, amma ni da yake an dan kwan biyu da shigar, daga wannan lokacin zuwa yanzu abubuwa sun dan caccanja. Da dai idan ka zo ka sami darakta ko Allah ya sa ka fada hannun furodusa, ka yarda za ka yi kuma aka kakkawo wadanda suka yarda naka shikkenan. Yanzu ba hali mutum ya ce kai tsaye sai an je an yi rijista, an je an yi wannan an yi wancen, toh mu da namu da irin na sa tsarin, shi ma dai sai an bi mataki-matakin, amma da bambanci da irin na yanzu ba. Toh an dan yi gwagwarmayar kuma falillahil hamdu an samu an haye, tunda gashi an shiga ana ta bada gudunmawa.
A can baya babu wata wahala da mutum yake sha wajen samun damar shiga masana’antar kamar yanzu kenan?
Kai! wahala kai! Ana shan wahala gaskiya, duk abin da baka san shi ba, dole ka sha wahala kafin ka san shi, tsarin ne irin na wancen lokacin dana wannan lokacin da bambanci, ai kamar ma a baya an fi shan wahala fiye da yanzu.
A wancen lokacin da za ki fara fim, shin kin samu wani kalubale a gida, kamar wajen iyaye lokacin da kika sanar musu kina sha’awar shiga harkar?
Ah! Kwarai kuwa ba karamin kalubale ba, babban kalubale gaskiya. Amma da ya ke da farko ni karance-karancen mujallar fim shi ya kwadaita mun son shiga harkar, kin san shi komai baya rasa sila. Toh1 ina tashi sai na rinka bin adireshinsu, a jikin mujallar fim, sabida a lokacin babu lambobin waya sosai ta hannu, dana fada na ce zan yi, wai! ai na sha magana. kusan abun ma da ya sa dole ma da har na fara na hakura kenan. Lokacin dana fara gaskiya ban yi wata fita da yawa ba fim dina na farko dana fara a wancen lokacin 2002 shi ne wani fim Kudura. Kullum aka tambaye ne fim din dana fara fitowa zan ce Kudura, domin anan na fara fitowa. Na fito a matar Sani Musa Me iska mijin Fati Muhammad, akwai Ali Nuhu dana lokacin yana saurayi haka, akwai Ahmad S.Nuhu a cikin shirin, akwai Maryam Mushakka, akwai Hauwa Ali Dodo, akwai Mama Dumba marigayiya, akwai Zulkifilu Muhammad Marigayi, akwai Aminu Ali Kwai a Baka marigayi, shi ne fim dina na farko.
An dan fara a shiga nan a fita nan maganganu kalubalen da kike fada su suka sa dole na hakura, an fuskanci kalubale sosai a gida kafin shiga. Toh! amma da yake Allah ya nufa akwai rabon sai an yi, toh kuma sai ga shi an sake dawowa. Har ‘yan uwa suna madalla da shi albarka har ma kara samun tagomashi da farin jini, ba abin da za mu ce da ‘yan uwa sai Allah saka da alkhairi, da ‘ya’yanmu, da ‘yan uwanmu, muna aikinmu a cikin goyon bayansu, babu wani matsala, amma dai da farko kam an sami kalubale.
Daga lokacin da kika fara kika bari, kawo yanzu da kika dawo, kin yi fim sun kai kamar guda nawa?
Babbar magana, gaskiya ba zan iya lissafa adadin fina-finan dana yi ba, dan shi wancen lokacin ma fina-finan ba wasu bane shi Kudura din ne, sai dan wasu da za ka fito dan irin ‘background’ din nan. Amma dai aikin da kayi daga 2011 zuwa yanzu shi ne aka yi aiki, daga 2011 zuwa 15, ina da ‘record’ dana rinka rubutawa, na rubuta sun kai kamar 150 zuwa 2015 fa.daga 2015 dai ban kara yin rubutu ba zuwa iyanzu. Kin ga daga 2011 zuwa 2015 an samu shekara biyar, daga 2015 zuwa 2022 an samu shekara bakwai, daga shekara bakwai baya zuwa yanzu ban yi rubutu ba, kuma kullum a cikin aikin ake. Kin ga a kalla fina-finan sun doshi dari bakwai 700 in ma ban zuba du ba kar na zuba da yawa.
Masu karatu za su so ki fada musu sunayen wasu daga ciki?
Akwai Giwar Karfe, Ranar Suna, Ruwan Zuma, Gidan Biki, Tsintuwa, Gidan Aro, Sai A Lahira, Uwa Tafi Uwa, Mai Goro shi nawa ne, Babu Maraya, na sha wuya a fim din Babu Maraya, dan Zamfara muka je muka yi shi. Akwai Mahaifiyarmu, akwai Sammace na Yusuf Dan kundalo, shi kuma Niger muka je muka yi shi, akwai Gaba Da Gabanta, shi kuma mun yi shi a Kaduna, da dai sauransu ba zan dai iya tunawa ba, sai kuma daga bisani aka zo aka yi Siris fim dinnan, kafin mu fara shirin Dadin Kowa akwai wani na ‘Yan kudu da muka rinka yi na AHIF, wani ‘series’ ne, a shi na fara yin ‘Series’, bayan na Ahif din sai kuma na Dadin Kowa na Arewa 24, shi ne wanda na ci sunan Maman Haider, a Dadin Kowa na farko kenan, sai ‘Yan Zamani na tashar Dadin kowa. Bayan nan sai muka zo muka yi Labarina kusan mune muka fara Labarina, su ne dai ‘Series’ na dan farko-farko kenan. Shekara bakwai da ta wuce, sabida Labarina mun fara shi tun daga 2015 ba a haska shi da wuri bane sai wajen 2018 – 2019. Siris na lokacin nan da ake ta yi ba za su lissafu ba, amma zan iya dan tsinto kadan daga ciki, akwai; Amanar So, na kamfanin Ali Rabi’u Ali Daddy, akwai So Dangin Mutuwa, na Aminu Alrahus707.
Sai kuma muka zo muke ta yin ‘series’ din nan Uku Sau Uku, Kishiyata, Bakar Kasuwa, Zaluma, Halak, Baba Audu, Jawahir muna cikin daukarsa a yanzu haka mun yi ‘Season’ 1, muna dab da shiga Sizin 2. Akwai wani ma da muke cikin daukarsa Rudani, na Garzali Miko. Gasu nan dai ba za su fadu ba, abun ne da ka ake fada sai wanda Allah ya sa ya fado a bakinka.
A gaba daya fina-finan da kika yi, wanne ne kika fi so, ya zamo bakandamiyyarki a kaf! fina-finan da ki ka yi, kuma me yasa?
So so ne, masu iya magana suka ce sonkai ya fi. Gaba daya fina-finan dana shirya kamar yadda na ce miki akwai Mai Goro, Mahaifiyarmu, Dan Zaman Daki, me Goro nawa ne na kaina, amma babu sunana ko daya ban bawa kaina kiretit ba. Mahifiyarmu ni na shirya komai da komai shi ma ban bawa kaina wani suna ba, kawai dai na fito a aktires. Dan Zaman Daki ma ni na shirya komai da komai amma ban bawa kaina Kiredit ba. Fim din dana tsaya tsaiwar daka na bawa kaina sunan da ya kamata, magana ta Allah shi ne Attajira. Attajira shi ne bakandamiyata, ina son Attajira gaskiya.
Wanne bangare kika fi karkata a fina-finan da kike fitowa?
Babu wani maganar karkata, kawai aktin ne duk wanda ya biyo ta kanka za ka yi su, amma ni dalilin da mutane ya sa ma suke ce mun Uwa ta gari, sabida na fi fitowa a Uwa. Za ki ga na fito da ‘ya’ya ba miji, galibi irin daga ni sai ‘ya’yana irin miji ya mutu ko Mata haka ko Maza.
Toh shiyasa duk randa aka ce an dan yi wani abu, kamar ko na rashin tausayi, ko na rashin kirki sai ki ji mutane suna ta ‘yan maganganu amma na dan yiyyi shi. Sai dai wanda za a fito ana nasiha na tausayi gaskiya ya fi yawa, dan sabida shi ne ma yawansa ya sa na goge, dan idan wani abu ya kama na kukan yanzu-yanzu sai ki ga ina kuka. Toh! gogewa ne da wancen rol din da ake bani na tausayi dani da ‘ya’yana ko ba mu da komai, irin kakani kayin talauci ana fama yarkace yarkace da rayuwa.
Yanzu ace kina bibiyar Uku Sau Uku kamar irinsa ya fi rinjaya. Amma ba ni ce na fi rinjaya kaina ba, masu bayarwar ne suka fi rinjayani a haka. Amma kuma ana bani, in kika duba Uku Sau Uku akasin haka kina duba Kishiyata za ki ga shi kuma irin abin da nake yi a Kishiyata daban.
Toh! irin wannan na yiyyi su, ba ma zan iya lissafasu ba. Kamar lokacin da muka yi Sammace, ai high killer nake daukowa na ce aje a kashe yarinyar, sabida da ‘ya ta ake so Fati Washa, sai kuma ya tafi ya fara son wata yarinya a Niger, toh Niger din ba ma garinmu ba ne Niger din bin bayan ‘ya’yanmu muka yi, amma a can har na samu sarari nake neman Haya kila su je su kashe mun yarinyar.
Nayi wani fim na Atete ‘KI JE KYA GANI’, shi ma in da nake yi wa dan kishiyata Asiri, haka dai karshe dana ne yake tsallakawa, Ki je kya Gani ma an taka Muhimmiyar rawa gaskiya ta rashin Kirki. Kamar Labarina shi ma da ni aka fara, ni ce kusan biliyon din ma da suka tsinci kansu muka je uwar ba lafiya ni da kaina muka kama uwar da Nafisa muka je muka sa ta a mota, na kuma dawo na shi ga dakin na kwashe kudinsu kaf!, na ce na debi kudin hayata, in ma ta mutu ta je ta karata, ko ‘ya ta ci gaba da zama dai na debi kudin hayata.
Kin ga kamar fim din Yankan Kauna shi ma an rufe ido da yawa gaskiyar magana ai kuwa an sha surutu, dan kuwa Yankan Kauna ma ba laifi gaskiya. Ire-iren hakan dai an yi su da yawa sosai ma kuwa. Toh! amma da yake wannan din ya fi rinjaya shiyasa an fi ganin abun tausayin in kai wancen din ma, sai a rinka ganin wani abu daban an canja maka rol. Ba ni ce na fi karkata ba, su ne dai suka ga suna samun abin da suke so ta wancen bangaren, amma duk bangaren da aka baka kana yi in sha Allah.
Wanne rawa kika taka a cikin shirin Yankan kauna da har mutane ke magana akai?
Rawar dana taka a shirin shi ne; na uwar miji, dana ne Ibrahim Maishunku, yake auro yarinya salaha me kyautata mana, mutuniyar kirki, Sha’awa ga rai ga idanu, na dau kahon zuka na tsani yarinyar nan, shi ma miji muna tare da shi Allah ya rahma masa Bankaura shi ne mijin, shi ma na cuccusa masa ra’ayi muka hadu muka tsani yarinyar, shi gaskiya ra’ayi aka cusa masa, karshe dai har sharri muke wa yarinyar, mu hada baki da wani yaro ya zo ya shiga bangarenta, bayan tana da ciki na je na kada mata magani na bata ta sha, tana murkukusun ciwon ciki aka zo aka saka mata yaro ba ta sani ba.
Muka kira danmu muka ce ya zo ya ga irin abin da take yi, yana shigowa yaron yana fita da gudu, muka ce “ka gani da idanunka ko? toh kana tafiya haka take kira ho wanda ta ga dama su zo su shige daki ba mu san karatu suke koya mata ba me suke koya mata oho!”. Toh! shi ne ransa a bace yana fadawa daki ya sameta tana murkukusu bai ji tausayinta ba yayi mata sha tara ta tsiya.
Kuma ga ta ba ta da gata, ba ta da kowa, shi ne ya aurota ba ma musulma bace ya musuluntar da ita, muka tsaya tsaiwar daka muka tsaneta, sai da muka sa ya sake ta. Inda za a yi tsiyar shi ne na je na sa ya auro ‘yar aminiyata wato Jamila. Karshe dai Jamila Allah ne ya taimake ni ta wankan mari ne kawai ba ta yi mun ba, amma fitsara ta rinka sarbada mun ita har kala mana sata tayi.
Toh a fim din Yankan Kauna ne sai gani dumu-dumu har da ankwa ne aka samun ne ko kuma motar ‘yan sanda ce ne aka zo aka tafi da mu, aka ce ana tuhumar mu da sata, ta ajjiye kayanta mun satar mata, ko sarkar kwal ce? na dai manta mun satar mata. Bayan Yankan Kauna akwai wani da shi ma nayi Biyayya, yaron yana da masifar biyayya shi ma haka na dinga uzzurawa matarsa.
Dan akwai ranar da ya taho da huluna an sha dariya a wannan wajen, huluna ya karbo daga gurin wanki, ya zo daf-daf zai shige wajen matarsa na ce “Toh bakin algungumi na ganka, Au! shi ne ka siyo mata nama lodi guda a leda, shi ne ka zo kake lallabawa kake satar hanya za ka shige ka kai mata ‘yar mayu ta ci, ni ga tsohuwar banza na haifi namiji.
Da ma da ka haifi namiji, wallahi tallahi namiji ba shi da imani”, na dora hannu aka, ya ce “haba! Mama dan Allah Hajiya ki yi hakuri, kin gani wallahi huluna ne na karbo daga wajen wanki” , sai kuma nai kwatages, na ce “ai na sani kun iya munafunci za a munafunce ni”.
Toh! shi ma dai haka, irin wannan dai akai ta fama, karshe dai na sa aka sake ta aka auro wadda nake so, ita kuma ta rinka casa mun rashin mutunci, har barkono take zuba mun a buta na zo zan yi alwala kawai na ji ashe barkono ta zazzaga a cikin butar, ta jefar da bahon ayaba na taka na zame, na balle a kafa aka zauna akai ta jinya. Irre-irrensu an yi su da yawa, Allah dai ya rufa asiri.
Ya kike cin karo da masu kallo, musamman yadda kike fitowa a wasu fina-finan matsayin uwar miji mara kirki, me kuntatawa, shin ba kya fuskantar wani kalubale daga gare su, musamman lokacin da kika fita gari dan yin uzurinki?
Eh! toh, ana samun maganganu sosai, za ki ji mutane suna cewa “Ya kuma muka ganki a haka?” Sabida an saba ganin na fito a me kirki. Dan bana mantawa a lokacin da na yi labarina sanda ya fito, wallahi wani yaro da gaske ya kira ni kamar zai yi kuka, saboda yana masifar kaunata ya ce “Haba Mamanmu, haba Hajiya, ya ya akai aka yi haka?, kina abubuwanki muna jin dadi, kina abubuwanki na tausayi na jan ‘ya’ya a jika, ya akai wannan karon kikai wannan? kai.. Amma dai wannan an yi rashin tausayi^. Kuma ban san shi ba kawai dai ‘fans’ ne, na ce “Kwantar da hankalinka dana ai fadakarwa ce, kuma shi cikar jarumi shi ne duk inda aka lankwasa shi ya juyu, duk sanda aka ce mutum abu daya zai ta yi ai sai ya gundure shi’. sannan ya ce “eh! haka ne”. Amma ana dan yin maganganu, yanzu kin ga irin maganganun da ake sha akan Kishiyata kuma inda na gode na ji dadi, sai abubuwan suke tafiya kusan lokaci daya, can UKU SAU UKU kana kallona na sha kuka na jeme na yi jemai-jemai ni da ‘ya’yana. Kana shi ga kishiyata sai ka ga akasin haka toh shi ne aktin din.
Mu koma baya kadan, me ya fara baki wahala lokacin da za ki fara harkar fim, ksancewar lokacin shi ne farkon farawarki?
Kin san shi abu sawa ne a rai, wani za ki ga yana son abun amma ransa bai karba ba, muna ta fama da irin wadannan har i-zuwa yanzu dinnan. Amma ni a lokacin da yake na riga na sa a raina, ina son zan yi abun, Allah ya sani ni ban sami wata wahala ba, ba wata wahala da na sha, kuma jaruman da ake yayi a lokacin a cikinsu aka tsundumani. Shi kansa Daraktan Allah ya rahama masa Tijjani Ibrahim, bana gushewa duk sanda zan yi hira sai na ambaci sunansa da alkhairi. Lokacin ya ce mun “Kai kin ga da na je gida na sa ‘prebious’ din wannan, haka na cewa matata wannan fa sabuwa ce”, ta ce “kai! amma wannan gaskiya za a dade ana yi, gaskiya tayi kokari, yanzu wannan na farko ne?”. Ban samu wata matsala ba a satin da na je, a satin akai kastin dina a fim din Kudura, da yin fim din da rasuwarsa bai fi watannu ba, Allah ya ji kansa ya rahama masa.
Bayan da kika tsunduma cikin harkar gadan-gadan, ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta game da fim?
Eh! gaskiya a cikin harkar mu ta fim, akwai kalubale, muna fuskantar kalubale sosai, saboda tunda nake ganin harka ta rayuwa ban ga harkar da take da raina matsayi irin harkar fim ba. Wato duk kokarinka idan kai ba wani bane, ta bakin bahaushe idan ka ji an ce yabon dan birni in aka ce wani shege, wato wani kasaitacce kenan, in kai ba wani shege bane kai kawai gaka nan ne. Za mu je ‘location’ saboda a cikin harkar nan tamu, wadanda ake jin maganarsu ko suke fada a ji, Maza dai suna daga ciki, akwai wasu daga manya iyaye ba da yawa ba, Maza Jarumai, sai ‘Yan Mata Jarumai. Toh! mu kuma gaskiyar magana mu iyaye mu ne mi’ara koma baya, gaskiya ba mu wuce ‘yan rakiya ba. A cikinmu ba su da yawa wadanda suke magana ake jin maganarsu ko ake girmamasu, wannan ba karamin kalubale bane, muna fuskantarsa. Sai kuma a kan su masu shiryawar Furodusas din, su ma akwai lokacin da suke ba da matsala.
Kin ga kamar a cikin jarumai akwai wanda ba ma zai zo aikin ba sai an tura mishi kudin aikinsa, amma akwai wanda sai ka gama ka yi ta jira ba a maida hankali an baka ba, wani ma ya ki biya, wani ko ka yafe masa Allah ba zai yafe masa ba, saboda an zalunce ka. Ba zan manta ba akwai aikin dana taba zuwa wajen 2013 aikin Babu Maraya zai kai wajen shekara tara, muka je Zamfara akwai kudi a jikina kusan dubu ashirin 20,000, a aikin nan sai da ta mutu. Na je muna aikin aka ce za a kwana biyu ba a taba bangarena ba, na ce toh! ina da aiki a Kano na dawo Kano, na zo na yi wani aikin na koma Zamfara, na je muka karasa aikin, muna Zamfara akwai aikin da aka kira ni kuma babban aiki ne, saboda wannan aikin na Zamfara wallahi haka na ce ina aiki, ban samu zuwa ba.
Na kuma wuni kwana biyu ba komai ina zaune, a inda muka sauka ni nake cira kudina ina siyen abinci har yaran ma da aka barni da su ni nake cire kudina na siya mana abinci. Aka gama aikin nan aka sallami kowa dan tahalikin nan ni bai sallame ni ba, shike nan amma saboda yana da kima a idanuna na ce to ni ba zan ci gaba da zama ba kowa ya tafi, ai ba zan zauna saboda kudi ba, in muka zo Kano ma hadu. Na kamo hanya na taho Kano, yana zuwa ya tarar na tafi ya kira ni a waya “Mama ya akai haka kuma na zo ban same ki ba Hajiya”. Na ce “Laah! kar ka damu babu wani abu za mu hadu a Kano”, ya ce “toh Allah baki lafiya”. Haduwar da ba mu yi ba kennan ta dai wannan kudin, in muka hadu da shi ma sai ya dan buya, tun yana dan gudu yana dan buya toh dai kawai ya fuzge ina wuni, ina gajiya, mu gaisa, ya ci gaba da sabgarsa. Wai bawan Allahn nan bai tuna wannan abin ba sai bara, ba a shekara ba wallahi sai ya kira ni a waya “Oh! Hajiya nine wanne aiki ma muka taba yi da ke ne, kamar ban biya ba, dan labari nake babu me bina bashi, shi ne na tuna kamar ban biya ki kudinki ba”. Na ce “Au! ka ma manta wanne aiki ne? ai ni ban manta ba BABU MARAYA ne”.
Da wani ma sunan labarin ya kira na ce “a’a ni ban manta ba”na ce “kuma ni na yi surutun duniya wanda zai koma kunnenka kuma na san ka ji, baka ce komai ba, kuma na tattara na bari”. Ya ce “Da wacce niyya?” na ce ‘Na barwa Allah”. shi ne ya ce na turo ‘account number’ ya bani. Abin da zai baki mamaki dana tura account din sai ga dubu goma, dubu gomar ma ba gaba daya ba. Kuma ya kira ni wai na ga sako na ce na gani, wai “toh kuma Hajiya ai sai ki kira ki ce kin gani” na ce “toh ai ni ban ga abin da zan batawa kaina lokaci wajen magana ba, ba dai kasa ba na kuma gani?”. Na ce “wannan shi ne kake tunanin ka saukewa kanka nauyi?” na ce “toh Allah ya kyauta”. Wallahi wallahi akwai yarinyar da kawa ta yi dan a fim din akwai Fati Ladan, akwai Fati Washa, akwai Al’amin Buhari, akwai Ali Nuhu.
Wallahi wallahi nake fada miki yarinyar da ta yi kawar Fati Ladan wata yarinya Safiya ko? ‘Scene’ biyu ta yi cewa ta yi abin da aka ba ta dubu goma sha biyar 15,000, kawa ta fito amma ni ce uwar dan yana karami in kika ga yadda abin yake, tun daga karatun ‘script’ na fara kuka, saboda labarin. Mu ne na kauye da yaron muke tahowa da shi yana karami, wallahi abin gwanin ban tausayi, na je kuma a inda muke barin garin za mu je mu hau jirgin kasa, wallahi bayan wata itaciya dana bi sai da kaya ta yage ni a fuska, na zo wani ‘step’ da muke hawa a gurin dai muke tafiya mu zagayo kafin mu zo inda za a kashe mijina a tashar jirgin kasa, wallahi da na yi wata tuntsira gudi-gudi ga tsakiyar rana hannuna ya daki, ga gurin kwalta zafi, wani bawan Allah cewa yake “Sannu bayin Allahn nan haka kuke shan wahala?” Wai bawa bai baka kudinka ba sai bayan shekara takwas ya tura ma dubu goma, Allah ya kyauta.
Kenan maganar da ake yi a baya na cewar ana biyan ‘yan fim duba biyu wasu na karyatawa, hakan kenan tana faruwa ba wai kage ne aka yi musu ba?
A’a! akwai bambanci gaskiya, wani bai fi ya fito a Kaka ko Uwa ba, wanda bai fi ya yi ‘scene’ biyu ko uku ba, ko makamancin haka, ba kamar yadda za a ja fim tun daga farko tare da mutum har karshe ba. Ni na yi bayani ne a kan irin kamar raina mu da ake yi, da gangan ake raina mu, sai a nuna wani ya fi wani, amma ba wai irin wannan dan biyan uku da sisin ba. In za a biya ai ana biya, amma kuma wani sai ya rainaka. Akwai wadanda su ba ma za su fara ba sai an basu kudinsu ‘already’. Abin ya sha bamban da bayani na dana Ladin Chuma, saboda tsarin ba iri daya bane.
Toh ya batun Nasarori fa, wanne irin nasarori kika samu game da fim?
Alhamdulillahi masha Allah, ba abun da za a ce sai godiya, akwai nasarori, tunda duk harkar rayuwa dole akwai irin nasibin da take tattare da shi, wannan sanin fuskar gaskiya akwai alfarma a ciki. Za ka je guri akwai mutane, amma ana ganin fuskarka an sanka toh za ki ga ana haba-haba da kai, akwai alfarma ba karamin nasarori aka samu ba. Sanadin fim din nan mun samu abubuwa wanda ba za su iya ma lissafuwa ba, kuma na alkhairi, ba abin da za mu ce da harkar hausa fim sai godiya da fatan alkhairi. Yanzu kamar wannan hirar da muke da ke kin ga ai ita ma nasara ce, saboda ba dan ina harkar fim din ba ai kin ga ba za ki so ma ki yi hura da ni ba. Kasancewa ta na jaruma wadda kuma harkar take yi da ni akwai nasarori, za ki ga wancen rediyo buri ake ayi dan hira da kai, wannan radiyo so take tayi hira da kai. A tsakankanin nan a cikin sari sai da nayi hira da rediyo biyu, nayi hira da rediyo a wannan makon, wani sati na kara hira da wata rediyon, wannan ba karamin nasara bace. Kuma ina jin hira da ‘radio’ na kai sshekara bakwai ina hira da rediyo. Kuma kamar Kundun Kannywood wannan dama shiri ne namu, dan mu aka bude shi, ina jin kusan ni ce uwa ta farko da aka fara yin hira da ni, shi ma shekara wajen takwas kenan. Wannan ma ba karamar nasara ba ce. Kin ga tsakanin radio, Telebision, Mujallu, na yi hira tafi kala goma, kin ga ba dan kasancewar Jarumar ba wadda kuma harkar take dan tafiya da ni kin ga ba wanda zai nemi ya ji ta baki na…
Za mu ci gaba mako na gaba in sha Allah_