ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hare-haren ‘Yan Bindiga: Za Mu Raba Tallafi Ga Mutanen Da Abin Ya Shafa A Katsina – Ministar Jinkai

by Sulaiman
4 years ago
'Yan bindiga

Gwamnatin Tarayya ta fara tattara sunayen waɗanda hare-haren ‘yan ta’adda ya shafa a wasu ƙananan hukumomi a Katsina.

Aikin tantance sunayen wanda ake gudanarwa a ƙarƙashin Ma’aikatar Ayyukan Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa wadda Hajiya Sadiya Farouk ce Minista, zai ɗauki sunayen ne daga ƙananan hukumomi 11 domin su shiga cikin tsarin masu cin gajiyar shirye-shiryen da ma’aikatar ke samar wa marasa galihu a faɗin ƙasar nan.

ADVERTISEMENT
  • ‘Yansanda Sun Harbe ‘Yan Bindiga 2 A Jihar Katsina

Jagorar tawagar da ma’aikatar ta tura Katsina domin wayar da kan jama’a dangane da shirin ce ta bayyana haka.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Nadia Muhammad ta ce, ”waɗanda hare-haren ‘yan bindiga ya shafa su na cikin wani halin da su ke matuƙar buƙatar samun tagomashin canjin rayuwa.”

Daga cikin tsare-tsaren da za a saka sunayen waɗanda za a tantance ɗin har da shirin bayar da tallafin kuɗaɗe ga marasa galihu, shirin bayar da jarin tallafawa domin a yi ƙananan sana’o’i, shirin N-Power, shirin ciyar da ɗalibai da sauran su.

Da ta ke jawabi, Funke Olatunji wadda ta wakilci Shugabar Sashen Ayyukan Musamman a ma’aikatar, wato Nadia Muhammad, ta ce matsalar tsaro ta kawo cikas sosai wajen kasa kai kayan agaji da gudanar da ayyukan jinƙai a wasu yankunan karkarar da ‘yan bindiga su ka addabi jama’a da dama.

“Dalilin haka ne wannan ma’aikata ta fito da shirin tantance sunayen domin su riƙa cin moriyar ayyukan wannan ma’aikata kai-tsaye,” inji ta.

Daga nan ta gode wa Gwamnatin Jihar Katsina dangane da ƙoƙarin da ta ke kan yi wa waɗanda hare-haren ‘yan bingida ya shafa.

Wasu da hare-haren ‘yan bindiga ya shafa daga ƙananan hukumomin Jibia, Batsari da Kurfi, sun shaida wa jami’an shirin cewa su na buƙatar muhalli.

'Yan bindiga
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Akwai Raini Da Nuna Bambanci A Masana’antar Kannywood —Maman Haidar

Akwai Raini Da Nuna Bambanci A Masana’antar Kannywood —Maman Haidar

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.