Jami’an tsaro a Nijeriya sun kashe ‘yan fashin daji takwas tare da ƙwace babura yayin wani samame da suka kai a yankin Chikun da Birnin Gwari na Jihar Kaduna, a cewar gwamnatin jihar.
BBC ta rawaito cewa, Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya ce dakarun rundunar rundunar haɗin gwiwa na Operation Forest Sanity ne suka ƙaddamar wa ‘yan bindigar cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma’a.
“Dakarun sun gwabza da ‘yan fashin kuma suka kashe takwas daga cikinsu, sannan suka ƙwace babura huɗu da wayoyin hannu a samamen farko,” in ji shi.
Jami’an tsaron sun sake karawa da ‘yan bindigar a karo na biyu kuma suka ƙwace babur biyu.
A gefe guda kuma, dakarun sun yi nasarar kashe wasu ‘yan fashi biyu a yankin Sabon Birni da Maidaro da Dogon Dawa, duka a Jihar ta Kaduna.
A wannan karon ma, jami’an tsaro sun ƙwace bindiga ƙirar AK-47 da kuma harsasai da dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp