Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta karbi wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP da jam’iyyar NNPP a jihar.
A ranar Litinin ne tsohon Gwamna kuma shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Abdul’aziz Yari ya karbe su.
- An Raya Hadin Gwiwa Bisa Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Yadda Ya Kamata A Shekarar 2022
- Masu Garkuwa Sun Kashe ‘Yan Gida Ɗaya Bayan Sun Karɓi Kudin Fansarsu Naira Miliyan 60
Mai magana da yawun Yari, Dahiru Mafara ne, ya bayyana sunayen mutanen a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Su ne Ibrahim Shinkafi, dan takarar Sanata na jam’iyyar NNPP mai wakiltar mazabar Zamfara ta Arewa; Dan takarar majalisar wakilai, Shinkafi da Zurmi, Suleiman Garba.
Ma’ajin Jihar, Suleiman Galadi; Su ma shugabannin NNPP na kananan hukumomin Kaura-Namoda da Zurmi sun sauya sheka.
Sauran sun hada da Kodinetan wata gidauniyar yakin neman zaben gwamna a jam’iyyar PDP, Aminu Kanoma, da kuma Sakatare kuma Ma’aji, Aminu Saminu da Hajiya Umulkhairi Aminu.
Yari ya samu wakilcin shugaban kwamitin tuntuba da wayar da kan jama’a na kwamitin, Musa Zubairu.
Taron wanda ya gudana a Talatan Mafara, ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na Zamfara, Tukur Danfulani da sauran masu ruwa da tsaki.