Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta amince da siyan dan wasan gaba na PSV, Cody Gakpo, akan kudi fam miliyan 35 da karin tsarabe-tsarabe na fam miliyan 10.
Gakpo, mai shekara 23 a duniya dan asalin kasar Netherlands ya zura kwallaye 13 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 17 a cikin wasanni 24 daya bugawa kungiyar ta kasar Netherlands.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ce dai take zawarcin dan wasan tun a cikin watan Agusta sai dai daga baya kungiyar ta sayi Antony daga Ajax.
Liverpool dai tana fama da ‘yan wasan da suke jinya bayan dan wasa Luiz Diaz ya samu ciwo a kwanakin baya kuma tun bayan tafiyar Sadio Mane kungiyar take fama da rashin cin kwallaye.
Liverpool dai tana mataki na 6 akan teburin premier league na Ingila maki daya tsakanin ta da Manchester United wadda take mataki na biyar.