Rundunar ‘yansanda a Jihar Anambra ta ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari a hedikwatar sashin Ihiala da bam da sanyin safiyar ranar Laraba.
Rundunar ‘yansandan ta ce ‘yan bindigar sun jefa bama-bamai a cikin ginin lamarin da ya sanya ginin konewa.
- Gwamnati Na Shirin Karawa Ma’aikata Albashi – Ministan Kwadago
- Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 7 A Neja
An ce jami’an ‘yansandan da ke wurin sun yi artabu da ‘yan bindigar tare da kwato bindiga kirar Ak-47 – amma masu laifin sun tsere.
“Jami’anmu da sanyin safiyar yau sun yi artabu da wasu ‘yan bindiga da suka kai hari a hedikwatar ‘yan sanda ta Ihiala suka kuma kwato bindiga kirar AK-47 guda daya,” in ji kakakin rundunar Tochukwu Ikenga a cikin wata sanarwa.
“’Yan bindigar sun tsere daga wurin ne saboda yadda jami’an ‘yansandan suka yi ta harbe-harbe duk da cewa ba a samu asarar rai ba.
“Abin takaici, bama-baman da ‘yan bindigar suka jefa a cikin ofishin ‘yansanda sun riga sun kone ginin.”
Harin dai shi ne hari na baya-bayan nan da ‘yan bindiga suka kai kan ofisoshin ‘yansanda da jami’an tsaro a jihar.
A watan Yuni, Leadership Hausa ta ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a hedikwatar ‘yansanda da ke Anaku, Anyamelum.
Yayin da ba a samu asarar rai ba a wannan harin, Ikenga ya tabbatar da cewa an kone motoci uku a harabar.
Watanni biyu kafin nan, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani shingen bincike na ‘yansanda a karamar hukumar Aguata, wanda ya yi sanadin jikkatar jami’ai uku.