• English
  • Business News
Saturday, May 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Gudanar Da Tsarin Jigilar Ruwa Dake Amfanawa Jama’a

by Sulaiman
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Sin Ta Gudanar Da Tsarin Jigilar Ruwa Dake Amfanawa Jama’a
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Abokai, ranar 27 ga watan Disamba na bana ne aka cika shekaru 20 da Sin ta aiwatar da tsarin jigilar ruwa daga kudu zuwa arewacin kasar. Gwamnatin Sin ta gudanar da wannan tsari domin daidaita matsalar karancin ruwa da sassan arewacin kasar ke fuskanta. Wannan tsari yana jigilar ruwan kogin Yangtze dake tsakiyar kasar Sin, wanda ya kasance kogi mafi tsayi a kasar, zuwa wuraren dake fama da karancin ruwa na arewacin kasar, ciki hadda manyan birane biyu wato Beijing da Tianjin da sauransu. An fara gina shi a ran 27 ga watan Disamba na shekarar 2002.

Tun lokacin da aka kammala gina sashin gabas da na tsakiya na wannan aiki a shekarar 2014 zuwa yanzu, an yi jigilar ruwan da yawansa ya kai cubic mita biliyan 58, tsarin dake amfanawa jama’a da yawansu ya kai miliyan 150 na gundumomi fiye da 280. Ban da wannan kuma, tsarin ya kawowa wadannan wurare babban moriya ta fannin tattalin arziki da kare muhalli.

Aiwatar da wannan tsari na da wuya matuka, amma gwamnatin Sin ta kammala shi wanda ya kasance daya daga cikin ayyuka mafi ban mamaki a duniya, duk bisa manufar “Jama’a gaba da komai”.

Jama’ar dake Beijing da Tianjin da dai sauran wurare a arewacin kasar, wadanda da ma suka dogara da ruwa daga karkashin kasa, yanzu suna amfani da ruwa mai tsabta da aka yi jigila daga kudancin kasar, ba tare da damuwa da matsalar karancin ruwa ba. (Mai zana da rubuta: MINA)

Labarai Masu Nasaba

Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo

Babban Bankin Sin Zai Inganta Hidimomin Kudi Don Habaka Amfani Da Shi

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 21, Sun Kama 780, Sun Kwato Makamai 1,408 A Kaduna 

Next Post

Qatar 2022: Za A Mayar Da Dakin Otal Din Da Messi Ya Zauna Wajen Tarihi

Related

Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo
Daga Birnin Sin

2 hours ago
Babban Bankin Sin Zai Inganta Hidimomin Kudi Don Habaka Amfani Da Shi
Daga Birnin Sin

Babban Bankin Sin Zai Inganta Hidimomin Kudi Don Habaka Amfani Da Shi

3 hours ago
Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani

4 hours ago
Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha

Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

11 hours ago
Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

13 hours ago
Next Post
Qatar 2022: Za A Mayar Da Dakin Otal Din Da Messi Ya Zauna Wajen Tarihi

Qatar 2022: Za A Mayar Da Dakin Otal Din Da Messi Ya Zauna Wajen Tarihi

LABARAI MASU NASABA

Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo

Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo

May 9, 2025
Babban Bankin Sin Zai Inganta Hidimomin Kudi Don Habaka Amfani Da Shi

Babban Bankin Sin Zai Inganta Hidimomin Kudi Don Habaka Amfani Da Shi

May 9, 2025
Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani

Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani

May 9, 2025
Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha

Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha

May 9, 2025
Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

May 9, 2025
Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

May 9, 2025
Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

GORON JUMA’A 09/05/2025

GORON JUMA’A 09/05/2025

May 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci