A gabannin sabuwar shekara ta 2023, wasu shugabannin kungiyoyin kasa da kasa kamar su hukumar kula da wasannin Olympics ta kasa da kasa, da asusun gina karfin nahiyar Afirka wato ACBF, da wasu shugabannin kafofin watsa labarai na kasa da kasa da suka hada da hukumar kula da kafofin watsa labarai na kasar Kenya, da gidan rediyon kasar Gabon sun aike da sakon murnar zuwan sabuwar shekara ga shugaba kuma babban edita na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG Shen Haixiong, inda suka nuna fatansu na ci gaba da kara zurfafa cudanya da hadin gwiwa dake tsakaninsu da CMG.
A cikin sakonsa, shugaban hukumar kula da wasannin Olympics ta kasa da kasa Thomas Bach ya nuna babbar godiyarsa ga shugaban CMG Shen Haixiong saboda goyon bayan da yake nunawa wasannin Olympics, da alkawarin da ya cika kan wasannin.
Shugaban zartaswa na asusun gina karfin nahiyar Afirka kuma tsohon mataimakin shugaban hukumar AU Erastus Mwencha ya bayyana cikin sakonsa cewa, yana fatan za a gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin asusunsa da CMG yadda ya kamata a sabuwar shekara dake tafe.
Babban jami’in zartaswa na hukumar kula da kafofn watsa labarai na Kenya David Omwoyo ya yi tsokaci cewa, yana fatan za a bude wani sabon shafi na hadin gwiwar dake tsakanin kafofin watsa labarai na kasarsa da CMG.
Haka zalika shugaban gidan talibijin na kasar Gabon Ali Reynald Radjoumba ya bayyana cewa, yana sa ran gidan talibijin din da CMG za su kara zurfafa hadin gwiwa a shekarar 2023 domin samun ci gaba tare.
A nasa bangare, shugaban CMG Shen Haixiong shi ma ya yi musu fatan alheri a sabuwar shekara, kuma ya bayyana cewa, babban taron wakilan JKS da ya kammala cikin nasara ba da dadewa ba, ya kara kuzuri ga hadin gwiwar sada zumunta tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya.
Ya kara da cewa, CMG yana son ci gaba da taka rawarsa ta kasancewa gada domin ba da gudummowarsa kan wanzar da zaman lafiya da samar da wadata ga al’ummar kasashen duniya tare da kungiyoyi da kafofin watsa labarai na kasa da kasa. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)