Yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Benin Patrice Talon sun aika wa juna sako domin murnar cika shekaru 50 da sake daddale huldar diplimasiya tsakanin kasashensu.
A cikin sakonsa, Xi ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru 50 da suka gabata, wato bayan da kasashen Sin da Benin suka sake kulla huldar diplomasiya a tsakaninsu, sassan biyu suna nuna wa juna sahihanci a ko da yaushe, kuma suna goyon bayan junansu a kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu duka. Ya ce yanzu ana gudanar da huldar Sin da Benin yadda ya kamata, haka kuma kasashen biyu sun samu babban sakamako yayin da suke hadin gwiwa a fannoni daban daban, kuma duk wadannan sun kawo moriya ga al’ummar kasashen biyu baki daya. Xi ya kara da cewa, yana mai da hankali matuka kan ci gaban huldar, kuma yana son yin kokari tare da shugaba Patrice Talon domin kara zurfafa hadin gwiwar kasashensu bisa shawarar ziri daya da hanya daya da tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, ta yadda za a ciyar da huldar Sin da Benin zuwa wani sabon mataki.
A nasa bangare, shugaban Benin Patrice Talon ya bayyana cewa, shi ma ya gamsu sosai kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a cikin shekaru 50 da suka wuce, kuma yana son hada hannu da shugaba Xi domin kara kyautata huldar Benin da Sin, kana yana cike da imani cewa, hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu zai ci gaba da samun babban sakamako. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)