Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammed Matawalle, ya tabbatar wa al’ummar mazabar Zamfara ta yamma cewa zai tabbatar gwamnatinsa ta gudanar da wasu ayyukan raya kasa.
Matawalle ya bayyana hakan ne a taron yakin neman zaben da aka gudanar a garin Bakura shalkwatar karamar hukumar Bakura ta jihar a ranar Laraba.
- Shugabannin Kungiyoyi Da Kafofin Watsa Labarai Na Kasa Da Kasa Suna Fatan Za Su Kara Zurafa Hadin Gwiwa Da CMG
- NIS Ta Bankado Sabbin Dabarun Da Masu Safarar Mutane Ke Amfani Da Su A Jihar Bayelsa
Gwamnan ya bukaci masu zabe da su zabe shi domin a ci gaba da gudanar da shugabanci na gari wanda zai iya sa jihar ta yi alfahari da shi wajen samar da ci gaban karkara da birane.
Ya umarci magoya bayan APC da su ci gaba da bin doka da oda domin gudanar da yakin neman zabe cikin lumana.
Ya yaba wa ‘ya’yan jam’iyyar APC bisa goyon bayan da suka bai wa majalisar yakin neman zabensa a Bakura, inda ya bukace su da su ci gaba da tafiya kafada da kafada don nasarar jam’iyyar.
A nasa jawabin shugaban kamfen na Matawalle kuma dan takarar majalisar dattawa mai wakiltar Zamfara ta yamma a APC, Alhaji Abdulaziz Yari ya bukaci ‘yan jam’iyyar APC da su zabi Bola Ahmed Tinubu da Matawalle da sauran ‘yan takarar jam’iyyar a zabe mai zuwa.