An kaddamar da aikin ginin tashar samar da lantarki daga hasken rana da karfin iska a hamada mafi girma na 7 a kasar Sin a jiya Laraba.
Tashar mai karfin KW miliyan 16, ita ce irinta mafi girma a duniya a yankunan hamada.
Kamfanonin kasar Sin da suka hada da China Three Gorges Corporation da Inner Mongolia Energy Group ne za su gudanar da aikin ginin tashar mai mazauni a hamadar Kubuqi dake jihar Mongolia ta gida mai zaman kanta a arewacin kasar.
Idan aka kammala, tashar za ta iya samar da wutar lantarkin da ya kai KWH biliyan 40 ga yankin Beijing-Tianjin-Hebei, a kowacce shekara.
Sama da rabin KWH biliyan 40 din zai kasance makamashi mai tsafta, wadanda ya yi daidai da ton miliyan 6 na kwal, tare da rage fitar hayakin carbon dioxide da kimanin ton miliyan 16. (Fa’iza Mustapha)