Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta fuskanci koma-baya a jadawalin kasashe mafi kwarewa a fagen kwallon kafa a duniya kamar yadda hukumar FIFA ta fitar da jadawalin a wannan mako.
 Kafin fitowar sabon jadawalin, Nijeriya na matsayi na 32 a teburin FIFA, sai dai kuma a yanzu ta koma na 35, sakamakon rashin zuwa gasar cin kofin duniya da kuma rashin nasara a wasannin sada zumunta.
 Kasar Maroko wadda ta yi rawar gani a gasar kofin duniya da aka kammala ba da jimawa ba a Katar, ta koma na 11 a duniya, sannan ta sauko da Senegal daga ta daya a teburin FIFA na mafi kwarewa a Afrika.
 Kafin a fitar da sabon jadawalin, Maroko na zaune ne ta 22 a duniya, yanzu kuma ta dawo ta 11 bayan da ta kafa tarihin zuwa zagayen kusa da karshe na gasar kofin duniya, wani abu da wata kasa a Afrika ko ta Larabawa ba ta taba yi ba.
Tawagar Super Eagles ta fuskanci koma-baya ne tun bayan gaza doke Ghana a wasan share fage na zuwa gasar kofin duniya, kuma hakan ya hana ta zuwa gasar ta Katar 2022 da aka kammala.
Kawo yanzu dai Brazil ce ke ci gaba da zama ta daya a teburin, Argentina da ta lashe kofin duniya ke bin ta, sai kuma kasar Faransa wadda aka doke a wasan karshe na cin kofin duniya take ta uku.