Kasar Sin ta fara aiki da wani babban layin samar da wutar lantarki, wanda zai rika samar da wutar lantarki daga yammacin kasar mai albarkatu zuwa yankunan dake gabashin kasar masu amfani da makamashi.
Rahotanni daga hukumar samar da wutar lantarki ta kasar Sin na cewa, an kammala aikin samar da wutar lantarki mai karfin kvt 800 na Baihetan-Zhejiang, kuma ya fara aiki Jumma’ar nan.
Za’a rika tura tsaftataccen wutar lantarkin da aka samar a Baihetan, dake zama tashar samar da wutar lantarki ta biyu mafi girma a kasar, daga lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar zuwa lardin Zhejiang dake gabashin kasar, ta layin da ya kai nisan kilomita dubu 2 da 121. (Ibrahim)