Kungiyar kwallon kafa da ke Kasar Saudiyya Al-Nassr ta dauki fitaccen dan kwallon kafar duniya, Cristiano Ronaldo.
Ronaldo ya kulla yarjejeniya da Al-Nassr har zuwa 2025.
- Likita Ya Yi Gargadi A Kan Tsaftace Kunnuwa Ta Hanyar Amfani Da Tsinke
- Sana’ar Hada Takalmin Silifas
Ronaldo ya rattaba hannun zama a kungiyar na tsawon shekara biyu.
Kungiyar za ta biyan Ronaldo €200 duk shekara, sannan za ta kulla yarjejeniyar kasuwanci tsakaninta da dan wasan.
Ronaldo dai ya raba gari da Manchester United a watan Nuwamba, lokacin da yake murza leda a Gasar Cin Kofin Duniya.
Ronaldo ya bar kungiyar ne biyo bayan wata hira da ya yi da ‘yan jarida inda ya soki kungiyar kan gaza samar da ababen atisaye na zamani.
Wannan hira ta tada kura a tsakanin mahukuntan kungiyar.
Ronaldo da kasarsa Portugal sun yi rashin nasara a hannun Morocco a matakin kusa da na kusa da karshe a Qatar da ci daya mai ban haushi.