Wasu mabiya darikar Shi’a sun gudanar da zanga-zanga a babban masallacin kasa da ke birnin tarayya, Abuja domin nuna adawa da hukuncin kisa da aka zartarwar da Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara.
‘Yan Shi’ar sun kuma nemi gwamnatin Jihar Kano, da ta gaggauta sakin Abduljabar tare da janye hukuncin da kotun shari’ar Musulunci ta zartar masa.
- Gwamnatin Kano Ta Tunbuke Kwamishinan Addinai Kan Rashin Mata Biyayya
- Sakon Sabuwar Shekara: Na Yi Iya Bakin Kokarina Wajen Yi Wa Nijeriya Hidima A Mulkina — Buhari
Masu zanga-zangar na dauke da kwalaye dauke da hoton Abduljabbar, sun gudanar da zanga-zangar ne a ranar Juma’a.
A wannan wata da muke cikin ne, wata kotun shari’ar Musulunci da ke jihar, ta yanke wa Abduljabar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsa da laifin batanci ga Fiyayyen Hallita Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.
Sai dai daliban Malamin sun lashi takobin daukaka kara kan hukuncin da kotun, karkashin jagorancin mai shari’a, Ibrahim Sarki Yola ta zartar masa.