A jajibirin sabuwar shekara ta 2023, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi domin murnar shiga sabuwar shekara, ta babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) gami da kafar yanar gizo. Ga Jawabin nasa:
Aminai da abokai, barkanku da war haka. Yayin da muke shirin shiga shekarar 2023, ina muku fatan alheri daga nan birnin Beijing.
A shekarar 2022, mun yi nasarar shirya babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20, inda aka tsara babban burin raya kasa ta zamani mai tsarin gurguzu daga dukkan fannoni, da sa kaimi ga farfadowar al’ummar Sinawa daga dukkan fannoni ta hanyar zamanintarwa irin na kasar Sin, lamarin da ya kara kuzari wajen kama hanyar sabon tafarki.
Kasar Sin ta ci gaba da kiyaye matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, wadda ta samu bunkasuwa yadda ya kamata, inda jimillar GDPn ta ta zarce kudin Sin Yuan traliyan 120 a duk shekara. Duk da cewa duniya na fama da matsalar karancin abinci, amma kasar Sin ta samu girbin hatsi mai armashi a cikin jerin shekaru 19 da suka gabata, lamarin da ya ba da tabbaci ga al’ummar Sinawa wajen samun isasshen abinci. Ban da wannan kuma, mun ci gaba da inganta sakamakon da muka samu wajen yaki da fatara, da kokarin farfado da yankunan karkara daga dukkan fannoni. Sa’an nan mun warware matsalolin da kamfanoni suka fuskanta ta hanyar rage kudin harajin da suke biya, baya ga taimaka wa jama’a wajen warware matsalolinsu.
Bayan barkewar annobar cutar COVID-19, ko da yaushe muna tsayawa tsayin daka kan fiffita muradun jama’a da rayukansu a kan komai, daukar matakan rigakafin cutar bisa ilmin kimiyya yadda ya kamata, da kuma kyautata matakan bisa sabon halin da ake ciki, hakan ya sa mun yi nasarar kare rayukan jama’a da lafiyarsu gwargwadon iko. Dimbin mutane musamman ma ma’aikatan jinya da masu aiki a sassa daban daban, sun yi namijin kokari wajen ayyukansu ba tare da tsoron wahalhalu ba. Abin farin ciki shi ne, a karshe dai mun haye wahalhalu da kalubalolin da ba mu taba ganin irinsu a baya ba. Gaskiya kowa jarumi ne. Yanzu mun shiga wani sabon yanayin rigakafin cutar COVID-19, kowa na ci gaba da kokarinsa, tabbas za mu samu nasara ba da jimawa ba. Jama’a, a kara kokari, idan muka dage tare da hadin kai, to za mu samu nasara.
A shekarar 2022, Marigayi Jiang Zemin ya riga mu gidan gaskiya. Ba za mu manta da babbar gudummawar da ya bayar da kuma da’ar da ya nuna ba. Za mu ci gaba da ciyar da sha’anin raya tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki zuwa gaba, kamar yadda Marigayi Jiang ya yi fata.
Tarihi bai boye kome ba, kasar Sin ta samu manyan nasarori a halin yanzu bisa gwagwarmayar da zuriyoyi daban daban suka yi.
Yanzu haka kasar Sin, kasa ce da ta cimma burika daban daban. Alal misali, kasar Sin ta samu nasarar shirya gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu da ta nakasassu, inda ‘yan wasannin kasar Sin suka lashe lambobin yabo da dama. An harba kumbunan Shenzhou 13 da 14 da 15 daya bayan daya cikin nasara, baya ga kammala aikin gina tashar sararin samaniya ta kasar Sin. A shekarar 2022, an cika shekaru 95 da kafuwar rundunar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin, dimbin jami’ai da sojoji na kara himma wajen raya sha’anin sojin kasar. Bugu da kari, an kammala aikin gina babban jirgin ruwan yaki mai daukar jiragen saman yaki kirar Fujian, an karbi babban jirgin sama kirar C919 na farko, kana an kaddamar da amfani da tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ta Baihetan. Dukkan wadannan nasarori na da nasaba ne da namijin kokarin al’ummar Sinawa da ba za iya lissafa su ba suka cimma. Wannan shi ne karfin kasar Sin.
Kasar Sin a halin yanzu, kasa ce mai kuzari. Yankunan gwaje-gwajen ciniki cikin ‘yanci, da tashar ruwa ta yin ciniki cikin ‘yanci ta Hainan suna bunkasa sosai, kana yankunan da ke gabar teku suna himmantuwa wajen yin kirkire-kirkire, yayin da yankunan tsakiya da yammacin kasar Sin suna gaggauta samun ci gaba, sa’an nan yankin arewa maso gabashin kasar ya kama hanyar farfadowa, an kuma wadatar da yankunan karkara a kasar, inda mazauna wurin suka kara samun kudin shiga. Tubalin tattalin arzikin kasar na juriya da kyakkyawar makoma da kuma kuzari cikin lokaci mai tsawo, bai sauya ba. Muddin muka kara himma da kokarin samun ci gaba, tabbas manufarmu za ta tabbata. A bana, na kai rangadin aiki yankin Hong Kong, inda na ji dadin ganin yadda kura ta kwanta a wurin. Tsayawa kan aiwatar da manufar “kasa daya amma tsarin mulki biyu”, zai wanzar da wadata da kwanciyar hankali a yankunan Hong Kong da Macao.
Kasar Sin a halin yanzu, kasa ce wadda ke gadar ruhun al’umma. Ba mu ji dadin aukuwar bala’u daga indallahi kamar girgizar kasa, ambaliyar ruwa, fari da gobarar daji da kuma wasu hadarurruka da suka auku ba. Amma yadda aka kokarta ceton rayuka da kuma taimakawa juna a wuraren da bala’u da hadarurrukan suka shafa, ya sosa rayukanmu sosai. Ba za mu manta da duk abubuwan da jarumai suka yi ba. A duk lokacin da muke dab da shiga sabuwar shekara, mu kan tuna da kyawawan halayyen al’ummar Sinawa wadanda muka gada daga kaka da kakani cikin shekaru fiye da dubu 1 da suka wuce, mu kan karfafawa juna gwiwar samun ci gaba.
Kasar Sin a halin yanzu, kasa ce da ke tuntubar kasa da kasa sosai. A shekarar da muke ciki, na karbi tsoffi da sabbin abokai da dama a nan Beijing, inda na bayyana ra’ayin kasar Sin game da harokin ketare. Duniya na samun sauye-sauye cikin sauri wadanda ba a taba ganin irinsu ba, har yanzu wasu sassan duniya na fama da rashin kwanciyar hankali. Amma har kullum kasar Sin na darajta samun ci gaba cikin lumana, da kuma abokanta da aminanta. Kasar Sin na nacewa gaskiya da adalci a tarihi da kuma ci gaban al’adun dan Adam, tana namijin kokarin ba da nata basira da shirye-shirye a sha’anin zaman lafiya da ci gaba na bil Adama.
Bayan babban taron wakilan JKS karo na 20, na je birnin Yan’an tare da abokan aiki na, inda muka waiwayi tarihin kwamitin tsakiyar JKS a birnin, wanda ba a taba ganin irinsa a baya ba, tare da kara fahimtar ruhun magabatan ‘yan jam’iyyarmu. Na kan ce, ba za a samu nasara ba, Sai an jure wahalhalu. A cikin shekaru fiye da 100 da suka wuce, JKS ta jure wahalhalu da dama, kuma tarihin JKS ya burge mu sosai. Wajibi ne mu yi gwagwarmaya, ba tare da jin tsoron kome ba, ta yadda kasar Sin za ta samu kyakkyawar makoma.
Kasar Sin za ta fito da abin al’ajabi ta hanyar yin gwagwarmaya. Shahararren marubucin kasar Sin Su Shi ya taba bayyana cewa, ba za a cimma buri mafi girma ba sai an jure wahalhalu masu wuya. Da kadan kadan matankadi ke shiga gora. Muddin muka yi aiki tukuru, tabbas manufarmu za ta tabbata.
Kasar Sin za ta samu karfi ta hanyar hada kai sosai. Kasar Sin, babbar kasa ce, mai mabambantan bukatu daga sassa daban daban, kana akwai bambancin ra’ayoyi kan wani batu, lalle hakan ba abin mamaki ba ne. Za mu cimma daidaito ta hanyar yin shawarwari da kuma tuntubar juna. Muddin mutanen Sin fiye da biliyan 1.4 muka cimma daidaito, muka hada karfinmu, to, za mu cimma burinmu, za mu kuma jure wahala. Wadanda ke zama a gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan, mu iyali ne. Ina fatan za mu hada hannu, a kokarin kawo wa al’ummar Sinawa alheri mai dorewa.
Kasar Sin za ta samu kyakkyawar makoma saboda ci gaban matasa. Kasar Sin ba za ta samu ci gaba ba, sai matasa sun sauke nauyi dake bisa wuyansu. Matasa cike suke da kuruciya, wadanda ake da kyakkyawan fata a kansu. Wajibi ne matasa su kasance masu kishin kasa, su yi gwagwarmaya don samun ci gaba, kar su bata lokaci.
A daidai wannan lokaci, wasu suna aiki tukuru. Ku fama da aiki, mun gode. A yayin da muke shirin shiga sabuwar shekara, bari mu jira hasken rana na farko a shekarar 2023, tare da kyakkyawan fata kan makoma.
Ina fatan kasar Sin za ta samu wadata da ci gaba da kuma kwanciyar hankali, inda kowa zai ji dadin zaman rayuwa! Ina fatan za a samu zaman lafiya da farin ciki da kwanciyar hankali a duniya baki daya. Ina taya ku murnar sabuwar shekara, kana kowa zai cika burinsa.
Na gode! (Kande Gao & Tasallah Yuan)