Tsohon Kwamishinan Harkokin Addinai na Jihar Kano, Dakta Muhammad Tahar Adamu, ya ce shi da kansa ya yi murabus ba tsige shi aka yi ba.
Idan dai za a iya tunawa dai, kwamishinan yada labaran Jihar Kano, Malam Muhammad Garba ne, ya fitar da sanarwa a ranar Asabar, inda ya bayyana korar Baba Impossible a matsayin kwamishinan harkokin Addinai.
- Abubuwan Da Suka Bambanta Harkar Fim Ta Da, Da Yanzu – Hajiya Zulaihatu
- Sabuwar Shekara: Sanwo-Olu Ya Yi Wa Fursunoni 104 Afuwa
A wata hira da ya yi da gidan rediyon Freedom a ranar Asabar, Baba Impossible, ya bayyana mamakinsa kan labarin korarsa da gwamnatin jihar ta fitar, inda ya bayyana cewa shi da kansa ya mika takardar murabus dinsa a ranar Juma’a, 30 ga watan Disamba, 2022 ga sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji.
Tsohon kwamishinan, ya ce ya yi mamakin jin a kafafen yada labarai cewa korarsa aka yi, wanda karya hakan.
Ya ce murabus din nasa ya samo asali ne bisa wasu dalilai na kashin kansa.
Baba Impossible ya ce gwamnatin jihar ta ci gaba da yin karya game da shi, amma ya ce hakan zai tilasta masa ya mayar da martani.
Sai dai a sanarwar da kwamishinan yada labaran jihar ya fitar, ‘’Korar kwamishinan harkokin Addinai na nan daram.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Korar da aka yi wa kwamishinan kuma dan majalisar zartarwa ta jihar ya biyo bayan halin rashin da’a ne a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati mai rike da mukami, da kuma kalamai marasa kan gado.”
Malam Garba ya yi nuni da cewa, an kuma same shi yana gudanar da al’amuran ofishinsa ne a matsayin wajen sana’a, har ma yana rage ranakun aiki ga ma’aikatan ma’aikatarsa, inda ya kebe ranakun Laraba da Juma’a.
Kwamishinan ya kara da cewa baya ga gudanar da aiki ba tare da tuntubar gwamnati ba, Baba Impossible baya biyayya ga gwamnati.
Ya bayyana cewa gwamnan jihar ya aike da sunan Dakta Nazifi Ishaq Bichi na Jami’ar Bayero Kano zuwa majalisar dokokin jihar domin maye gurbinsa.
Gwamnan ya yi wa kwamishinan da aka kora fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.