Dakarun ‘Operation Forest Sanity’ sun fatattaki ‘yan ta’adda hudu tare da kwato makamai da alburusai da sauran kayayyaki a arangamar da suka yi a Jihar Kaduna.
Manjo-Janar Musa Danmadami, daraktan yada labarai na tsaro ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.
- Ga Yadda Wasu Kasashe Suke Nuna Manufuncinsu Bayan Da Kasar Sin Ta Sassauta Matakan Kawar Da Cutar COVID-19
- Man U Na Shirin Yin Wuf Da Giroud Don Maye Gurbin Ronaldo
Danmadami ya ce a ranakun Lahadi da Litinin sojojin sun amsa kiraye-kirayen harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Rafin Sarki da ke karamar hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
Ya ce sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’addan ne tare da kashe guda biyu, inda suka kwato bindiga kirar AK 47 guda daya.
Ya kara da cewa a ranar Talata ne sojoji suka kai wani harin kwantan bauna a kauyen Rafin Taba da ke karamar hukumar tare da kashe ‘yan ta’adda biyu.
A cewarsa, sojojin sun kuma kwato bindigogi kirar AK 47 guda biyu, harsashin AK 47 guda hudu, alburusai 51 masu dangon 7.62mm, wayoyin hannu guda biyar, babura biyu da kudi Naira 206,000.
“Babban kwamandan sojoji ya yaba wa dakarun Operation Forest Sanity tare da karfafawa jama’a gwiwa da su bai wa sojoji sahihan bayanai kan aikata laifuka,” in ji shi.