Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin yin adalci ga kowa, idan aka zabe shi.
Tinubu ya yi wannan alkawarin ne a wani taro da ya yi da shugabannin Musulmin Arewa maso Yamma a Kano.
- Ana Sa Ran Birtaniya Za Ta Fice Daga Tsibiran Malvinas Bayan Daidaita Ikon Mallakar Tsibiran Chagos
- Gobara Ta Kone Shaguna 4 A Kano
Tinubu ya yi alkawarin yin adalci da bin ka’idojin Addinin Musulunci.
“Shugaba a jam’in sallah an umarce shi ya zama shugaban kowa. Idan aka zabe ni, zan yi mulki bisa gaskiya da dimokuradiyya, bisa tsarin mulkin kasarmu.
“Zan yi kokari na zama mai aminci kuma mai kwazo. Zan yi kokarin inganta rayuwar dukkan mutanenmu, Kirista ko Musulmi.
“Ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu damar haduwa da ku baki daya a wannan gagarumin taro.
“Ina addu’a Allah ya ci gaba da ba ku hikima da dabara don cika wannan babban aiki mai muhimmanci. Idan ba tare da jagorancinku da nasiharku ba, al’umma ba za su iya kai wa ga inda Allah ya nufe mu ba,” in ji shi.
Tinubu ya ce manufarsa, ita ce hadin kai, ci gaba da kuma daidaito don ci gaban Nijeriya.
Ya yi alkawarin farfado da tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa da rashin tsaro ta hanyar samar da kayan aiki na zamani ga hukumomin tsaro.