Pep Guardiola ya yi imanin cewa Man City sai ta nuna duk bajintarta kafin ta sha gaban Arsenal a gasar Firimiya.
City mai rike da kambun kofin zai iya zama tazarar maki biyar kacal tsakaninta da Gunners idan tayi nasara a karawarta da Chelsea a ranar Alhamis bayan Arsenal ta yi kasa da maki a wasan da suka tashi babu ci da Newcastle a ranar Talata.
“Dole ne mu rage rata tsakaninmu da Arsenal ta hanyar buga wasanni masu kyau da kuma samun nasara, amma fa su (Arsenal) suna da karfin gwiwa 100 bisa 100 idan suka cigaba da samun nasara a sauran wasanninsu.” Guardiola ya shaida wa taron manema labarai kafin wasan ranar Laraba.
“Dole ne mu buga wasanni masu inganci cikin nasara sannan kuma muyi fatan su samu tangarda a sauran wasanninsu. Duk da cewa, wasan da suka buga a daren jiya ya nuna cewa, har yanzu suna da kyau sosai. ”
Chelsea dai ta samu nasara ne sau daya cikin wasanni bakwai da ta buga a gasar Firimiyar amma har yanzu Guardiola yana sa ran karawarsa da Chelsea a filin wasa na Stamford Bridge zai iya zama mai kalubale.