Wata babbar kotu da ke babban birnin tarayya Abuja ta dakatar da bukatar tsige shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu daga mukaminsa bisa zargin kin bayyana hakikanin kasarorinsa.
Mai shari’a M.A. Hassan a ranar Laraba ya ki amincewa da bukatar tare da hujjoji 14 da masu shigar da karar suka kawo.
Alkalin kotun ya ce Farfesa Yakubu ya bayyana kadarorinsa akan yadda doka ta tanadar.
Ya hana jami’an tsaro na farin kaya (DSS), ‘yan sandan Nijeriya, da kuma kotun da’a (Code of Conduct Bureau) kama Farfesa Yakubu.
A karar da Somadina Uzoabaka ta shigar da babban lauyan gwamnatin tarayya da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, Farfesa Yakubu mai lamba FCT/HC/GAR/CV/47/2022 tana neman kotun ne da ta tilastawa Farfesa Yakubu sauka daga kan mukaminsa kan zargin kin bayyana kadarorinsa ta yadda doka ta tanadar.