Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin tarrayyar Nijeriya, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin sabuwar jami’yyar da ba za ta kai bantenta ba a babban zaben shekarar 2023.
Alhassan Ado ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels a cikin shirin siyasa a yau a makon da ya gabata.
Shugaban masu rinjayen wanda jigo ne a jam’iyyar APC ya kuma bayyana cewa tasirin jami’yyar bai wuce garin Zariya ba da ke Jihar Kaduna daga bangaren yamma, haka daga bangaren gabas kuma iyakacinta karamar hukumar Wudil da bai gaza tafiyar kilomita 42 daga birnin Kano ba.
Doguwa ya kara da cewa, babu wani abin cewa kan jami’yyar NNPP, domin kuwa sabuwar jam’iyya ce da ba za ta iya kai bantenta ba.
A cewarsa, ko a zaben shekarar 2019 da tsohon Gwamnan Rabi’u Kwankwaso ya ke cikin babbar jami’yya ta PDP sai da ya yi rashin nasara a hannun jami’yyar APC, don haka ba wani sabon abu ba ne ya kara yin rashin nasarar a 2023.
Ya ce, “A yanzu yana cikin wata karamar kungiyarsa da ta kasance mallakinsa da ya kirawota da suna jam’iyyar siyasa wacce tasirinta bai wuce Zariya ba daga yamma, haka kuma daga gabas tasirinta bai wuce karamar hukumar Wudil da ke Jihar Kano ba.
A karshe Alhassan Ado Doguwa ya sha alwashi a kan cewa jami’yyar NNPP za ta fuskanci babban kalubale daga APC a Jihar Kano da hakan zai sa ba za ta samu ko kujera daya ba a zaben shekarar 2023.