• Leadership Hausa
Friday, August 19, 2022
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Al'ajabi

Kotu Ta Daure Wata Mata Shekara 30 Saboda Ta Yi Bari

by Sulaiman and Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
in Al'ajabi
0
Mata
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Lokacin da Karen ta farka daga bacci a wani asibitin El Salbador, ta lura cewa an saka mata ankwa a hannu sannan kuma ga ‘yan sanda a gefenta.

“Akwai mutane da yawa a wurin kuma suna ta cewa wai na kashe jaririna kuma ‘sai na fuskanci hukuncin abin da na aikata’,” kamar yadda Karen ta shaida wa BBC.

  • Safarar Mata Zuwa Kasashen Larabawa Da Turai Ya Zama Ruwan Dare -MDD

Tana bukatar kulawar gaggawa saboda wahalar zubewar ciki. Amma Karen, mai shekara 22 a lokacin, ta tsinci kanta cikin zargin zubar da ciki.

“Na yi yunkurin yin bayanin abin da ya faru, amma suka ki sauraro na,” a cewarta.

Tsattsaurar Doka
El Salbador, da ke nahiyar Tsakiyar Amurka, na daya daga cikin kasashen da suka fi tsaurin doka kan zubar da ciki, wadda ta haramta duk wani nau’i na zubar da shi, ko da kuwa na barazana ga rayuwar mace ko an yi shi ta hanyar fyade ko kuma ‘yan uwa ne suka yi shi.
Karen, wadda aka tuhuma da kisan kai, an yanke mata hukuncin daurin shekara 30 a gida yari. Tana cikin rukunin mutanen da aka kira “Las 17”, wadanda aka taba yanke wa hukuncin dauri saboda yin bari ko kuma haihuwar jariri babu rai.

Labarai Masu Nasaba

Wani Mutum Ya Yanke Marainansa Yana Barci, Ya Dauka Nama Ne A Ghana

Mahaifiyata Ta Sare Min Hannaye Haka Siddan- Budurwa

Karen ta shafe shekara shida a garkame kafin daga baya a sako ta tare da wasu mata uku a watan Disamban 2021 sakamakon wani matsin lamba daga kasashen duniya.

A lokacin da aka tsare ta, Karen na da da mai shekara biyu. Karen ba ta sake ganin sa ba har sai da ya kai shekara tara.
‘Na so na rungume marigayin dana a hannayena’
Daya daga cikinsu ita ce Cinthya, wadda aka daure a 2009 kan kisan kai bayan danta ya mutu saboda an haife shi bakwaini. An sake ta a 2019.

Cinthya ta fada wa BBC cewa maimakon a nema mata motar daukar marasa lafiya, ‘yan sanda ne suka isa wurin. Ta sume, kuma ko da ta farka a asibiti, kamar Karen, sai kawai ta ga ankwa a hannunta.

An tafi da ita daga asibiti zuwa ofishin ‘yan sanda kai-tsaye kafin a fara yi mata shari’a. Ba a ba ta damar gani ko yin magana da ‘yan uwanta ba, hasali ma ko gawar dan nata ba ta gani ba. Shekararta 20 a lokacin.

“Na so na rungumi dana a hannuna, amma ba a ba ni dama ba. Haka ma ba su bar ni na je jana’izarsa ba,” in ji Cbthya.
Karen ta ce ta fuskanci irin wannan matsalar a kotu amma ta yi a cikin bursin saboda ta samu kanta cikin sauran matan da aka daure su bisa tuhumar zubar da ciki.

“Mu kusan 10 ne kuma wasu daga cikin matan sun fuskanci cin zarafi daga wasu fursunonin,” a cewarta.
“Daga baya sai muka kafa wata kungiya don taimaka wa junanmu.” Tasiri mara dadi.

Ba abu ne mai yiwuwa ba a iya cewa dukkanin cikin da suka zube ba matan ne suka zubar da su ba, amma masu fafutika na cewa dokokin na yanzu na daure matan da ba su zubar da cikin da gangan ba.

Masu kare hakkin mata a El Salbador na cewa lamarin ya fi shafar matan da ba su da arziki sosai da za su iya samun kulawa daga asibitoci masu zaman kansu.

Mata kamar Cinthya da Karen.
“Mata matalauta ne suka fuskantar matsala da irin wadannan dokoki da ke jawo musu tsana kuma suke sa wasu su aikata zubar da cikin,” in ji Morena Herrera, wata shahararriyar mai fafutika a El Salbador.

Cinthya ta yi ikirarin cewa lokacin da ake yi mata shari’a ba a bari ta yi magana ba a kotu. Haka nan, ba a bari an kai mata ziyara ba ko kuma yi mata bayani daga lauyan da gwamnati ta ba ta lokacin da take jiran shari’a a gidan yari. Ba ta ma san tuhumar da ake yi mata ba takamaimai. “Har sai a kotu sannan na ji cewa ana tuhuma ta da kisan kai,” a cewarta.

BBC ta nemi mahukuntan EL Salbador su mayar da martani game da zarge-zargen amma ba mu samu amsa ba. A cewar alkaluman wata cibiya da ke Amurka mai suna Center for Reproduction Rights, El Salbador na cikin kasashe bakawai a Tsakiyar Amurka da suka haramta zubar da ciki kwatakwata.

Honduras, da Jamaica, da Nicaragua, da Haiti, da Dominican Republican, da kuma Surinam ne sauran kasashen (a fadin duniya kuma, kasashen da suka haramta zubar da ciki kwatakwata 24 ne).

‘Wani kulli ne da ba shi da alamar warwarewa’
Har yanzu akan daure matan da suka yi bari a El Salbador. A watan da ya gabata ma an daure wata mace da aka bayyana da “Esme” shekara 30 a gidan yari. “Har ila yau ana daure mata irina a gidan yari. Wani kulli ne da ba shi da alamar warwarewa,” a cewar Cinthya.

Bayan an sako ta, Cinthya ta sha wahala wajen neman aikin yi saboda tarihin laifinta, amma sakamakon wani taimako da ta samu daga wata kungiya ta samu damar gudanar da harkokin sayar da tufafi.

Ta haifi wata yarinya a 2020 mai suna Marcela Elizabeth. “Na firgita lokacin da na samu ciki, saboda tsoron zan sake fadawa cikin abin nan idan aka samu matsala,” a cewar Cinthya.

“Amma an haife ta kalau ba tare da wata matsala ba. Ita ce farin cikina.”
Karen ta ce tana jin cewa mutane na nuna mata yatsa amma yanzu ta mayar da hankali kan karatun sakandare da ta fara a gidan yari da kuma sake kulla alaka da danta. Karen na ganin bayar da labarinta zai taimaka wa wasu matan.

“Har yanzu akwai abubuwan da ke damu na da ba zan manta da su ba. Amma magana a kansu za su iya taimakawa wajen dakile faruwar wasu abubuwan kuma ya taimaka wa wasu kawayena da har yanzu suke a daure.” Mun samu wannan rahoto daga BBC.

ShareTweetSendShare
Previous Post

Iyakacin Tasirin Jam’iyyar NNPP Wudil Da Zariya – Alhassan Doguwa

Next Post

Mulkin Dimokuradiyya Ya Kawo Ci Gaba Mai Dorewa A Gombe Da Nijeriya -Inuwa

Related

Wani Mutum Ya Yanke Marainansa Yana Barci, Ya Dauka Nama Ne A Ghana
Al'ajabi

Wani Mutum Ya Yanke Marainansa Yana Barci, Ya Dauka Nama Ne A Ghana

3 days ago
Mahaifiyata Ta Sare Min Hannaye Haka Siddan- Budurwa
Al'ajabi

Mahaifiyata Ta Sare Min Hannaye Haka Siddan- Budurwa

4 days ago
Dalibi Ya Daba Wa Wasu Dalibai 2 Wuka A Kan Musun Kwallon Kafa A Bauchi
Manyan Labarai

Saurayi Ya Babbake Gawar Budurwarsa Bayan Dirka Mata Ciki A Bauchi

5 days ago
Gajartar Amarya Tasa Ango Ya Fasa Auren Amaryarsa Ana Tsaka Da Gudanar Da Biki
Al'ajabi

Gajartar Amarya Tasa Ango Ya Fasa Auren Amaryarsa Ana Tsaka Da Gudanar Da Biki

6 days ago
Yadda Mai Wanke-wanke Ta Zama Mataimakiyar Shugaban kasa
Al'ajabi

Yadda Mai Wanke-wanke Ta Zama Mataimakiyar Shugaban kasa

7 days ago
Wata Sabuwa: Za A Fara Cin Tarar Mata Kan Kin Aure A Chadi
Al'ajabi

Wata Sabuwa: Za A Fara Cin Tarar Mata Kan Kin Aure A Chadi

1 week ago
Next Post
Mulkin Dimokuradiyya Ya Kawo Ci Gaba Mai Dorewa A Gombe Da Nijeriya -Inuwa

Mulkin Dimokuradiyya Ya Kawo Ci Gaba Mai Dorewa A Gombe Da Nijeriya -Inuwa

LABARAI MASU NASABA

Yadda Aka Sace Kwamishina A Nasarawa

Yadda Aka Sace Kwamishina A Nasarawa

August 19, 2022
Nadin Kwamishinoni A Kano: Kar A Yi Kitso Da Kwarkwata

Nadin Kwamishinoni A Kano: Kar A Yi Kitso Da Kwarkwata

August 19, 2022
Da Dumi-Duminsa: NBC Ta Soke Lasisin Tashoshin AIT, Silverbird TV Da Wasu 50

Da Dumi-Duminsa: NBC Ta Soke Lasisin Tashoshin AIT, Silverbird TV Da Wasu 50

August 19, 2022
srilanka

Darussa Daga Gwagwarmayar Kasar Sri Lanka (Nazari)

August 19, 2022
Goro

Goron Jumu’a

August 19, 2022
Nunez Ya Jika Wa Liverpool Aiki

Nunez Ya Jika Wa Liverpool Aiki

August 19, 2022
Kamata Ya Yi Dalibai Su Maka Kungiyar ASUU A Kotu Kan Bata Musu Lokaci—Adamu Adamu

Kamata Ya Yi Dalibai Su Maka Kungiyar ASUU A Kotu Kan Bata Musu Lokaci—Adamu Adamu

August 19, 2022
Kusan Shekara 100 Da Kafa Asibitin Kutare Na Kano, Amma…

Kusan Shekara 100 Da Kafa Asibitin Kutare Na Kano, Amma…

August 19, 2022
Son Zuciyar Wasu Tsiraru Ya Haddasa Rashin Tsaro A NIjeriya – Alhaji Ibrahim

Son Zuciyar Wasu Tsiraru Ya Haddasa Rashin Tsaro A NIjeriya – Alhaji Ibrahim

August 19, 2022
Kokarin CBN Wajen Daga Darajar Naira

Kokarin CBN Wajen Daga Darajar Naira

August 19, 2022
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.