Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sanar da dage yakin neman zabensa a Jihar Abia.
A cikin wata sanarwar da kwamitin yakin neman zaben dan takarar ya fitar, a yau Alhamis ya ce, Atiku ya sauya ranar da zai kaddamar da yakin neman zabensa da aka tsara za a gudanar a jihar Abia.
- A Matsayinta Na Kasa Mafi Yawan Masu Harbuwa Da Cutar COVID-19 A Duniya, Matakin Amurka, Tamkar “Barawo ke cewa ku tare barawo!”
- Da Dumi-Dumi: Sarkin Bauchi Ya Nada Sabon Waziri
A baya, an tsara za a kaddamar da yakin neman zaben a ranar 10 ga watan Janairu 2023, amma a yanzu an sauya ranar zuwa 9 ga watan Janirun 2023.
Sanarwar wadda daraktan kwamitin yakin neman zaben Atiku da Okowa da ke Jihar Abia, Kingsley Megwara, ya fitar ba ta ambaci daliban sauya ranar ba, amma ta nemi gafarar magoya bayan dan takarar da su yi hakuri a kan sauya ranar.
An dai tsara za a kaddamar da kamfen din a filin wasan Umuahia.
A kwanan baya dai, an ruwaito gwaman jihar Okezie Ikpeazu, bai halarci taron gangamin kaddamar da Atiku da Okowa a jihar da aka gudanar ba, ganin cewa, ya ci gaba da bin sahun kungiyar gwamnonin G-5 da gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ke jagoranta kan ci gaba da yin adawa da takarar Atiku.