Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Masatan Arewa Mazauna Legas, Alhaji Ibrahim Galadanci ya bayyana cewa dole ne gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele ya gurfana a gaban kuliya.
Shugaban gamayyar ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a makon nan.
Ya ce zargin da ake yi wa gwamnan CBN ya yi yawa kuma a matsayinsa na babban mutum da yake rike da ofis mai daraja a Nijeriya, domin ana zarginsa da almundahana da raba kudade ga ‘yan ta’adda da kuma rarraba kudade ba bisa ka’ida ba, bisa haka ne yake ganin ya kamata ya gurfana a gaban kotu saboda ya wanke kansa daga wadannan zarge-zarge idan har yana da gaskiya, idan kuma aka same shi da laifi a hukunta shi daidai da laifinsa.
A cewarsa, babu wanda ya fi karfin doka a Nijeriya, duk wanda ya karya doka idan har akwai adalci a gurfanar da shi a gaban kotu.
Ya kara da cewa akwai alamun kamshin gaskiya cikin wadannan zarge-zarge tun da majalisa ta kira shi ya ki zuwa, sannan Sanata Gudaji Kazaure ya fito karara ya fadi abubuwa a kansa kuma ya kamata a yi bincike a kan lamarin, idan har yana da hujjoji ba zai taba yarda wadannan maganganun su yi tasiri a kansa ba.
Alhaji Ibrahim ya ce hakki ne na shugaban kasa wanda ya nada Emefiele kan wannan mukami ya kafa alkalai da za su gudanar da bincike kan wannan zarge-zarge da ake yi masa.
Ya ce ya kamata shugaban kasa ya shiga cikin wannan zance gadan-gadan domin warware zare da abawa idan har yana son ceto Nijeriya, saboda kar ya tafi ya bar kasar da kura a kasa. Ya jaddada cewa wannan ba karamin lamari ba ne wanda ya kamata shugaban kasa ya yi rawar gani kan abubuwan da aka binciko kan lamari.
Shugaban matasan ya ce shugaban kasa a matsayinsa na adali uban kowa da kowa ne da ke kasar nan, ya kamata ya dauki mataki kan wannan zargi, domin mafi yawancin alkalan Nijeriya fuska biyu suke da shi, wanda shugaban kasa ya san da haka, ya kamata shugaban kasa ya kafa kwamitinsa wanda shi kadai za a bai wa sakamakon rahoton da aka bankado.
Ya ce kamar yadda ya rage saura kwanaki kalilan shugaban kasa ya bar karagar mulki, ya kamata ya san wani irin mataki zai dauka domin ya wanke kansa. Ya ce maganar ko kadan ba ta siyasa ba ce, akwai marasa kishin kasa shafaffu da mai masu yin amfani da kujeransu wajen lalata kasa a cikin gwamnatin nan.
Alhaji Ibrahim ya ce rawar da za su iya takawa a kungiyance shi ne, ci gaba da kiraye-kiraye har ya kai ga hunnun shugaban kasa domin ya dauki matakan da suka dace, saboda shi Allah ya bai wa amanar wannan kasa kuma zai tambaye shi yadda ya gudanar da shugabancinsa.
Ya ce mafi yawancin ‘yan Nijeriya na cikin wahala, tsirarun mutane ne suke jin dadi a kasar nan, kuma wannan ba karamin zargi ba ne wanda gwamnati za ta iya yin burus da shi.