A safiyar ranar Asabar da ta gabata ce, Mai Martaba Sarkin Dakwa Dakta Alasan Baba Chikuri, ya aurar da samari da ‘yammata 34, maza 17 mata 17, an gabatar da bikin ne a fadar sarkin da ke Dakwa ta yankin Karamar Hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
Bikin da ya samu halartar manyan baki daga sassan kasar nan.
Babban bako kuma uba a wurin shi ne, Tsohon Gwamnan Jihar Kano Kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, wanda kuma shi ya zama a matsayin uba ga ‘yammatan wanda shi ya ba da aurensu.
Wakilin LEADERSHIP Hausa Auwal Mu’azu, ya samu zantawa da Sanatan jim kadan bayan kammala daurin auren inda ya nuna godiya da farin cikinsa da zuwa wannan masarauta, musamman yadda ya ga an tsara gudanar da wannan aure. ” A yau wadannan mutum 34 za su kwana cikin farin ciki, da yawa mutane ba su gane fa’idar irin wannan aure a addinance ba, kuma basu gane shi a zamantakewa ba.
Yau sarki ya tuno min da wacan lokaci da muka yi auren maza da mata sama da dubbai, wanda yau din nan cikin yardar Allah.” In ji shi. Ya yi kira ga shugabanni da masu hannu da shuni da su yi koyi da irin wadannan abubuwan alheri.
A cewarsa wannan tsari ne da zai taimaka wa marasa hali su samu sukunin aurar da ‘ya’yansu, a karshe ya yi addu’ar fatan Allah ya sanya alheri ya kuma zaunar da su lafiya.
Tun da fari a nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Dakwa Dakta Alasan Baba Chikuri, godiya ya yi ga Allah bisa wannan rana mai mhimmanci, kazalika ya yi godiya ga jagoran na Kwankwasiyya bisa amsa gayyatarsa da ya yi, gami da yi masa fatan alheri da addu’ar Allah ya biya masa bukarsa na abubuwan da ya sa gaba.
Shi ma Sabon Sarkin Samarin na Dakwa wanda yana daga Abdurrahman Abdurrashid, wanda aka fi sani da suna Senior, a yanzu Alhamdu lillahi muna godiya ga Allah da ya sa muka kawo wannan lokaci, a yanzu dai an yi min sarauta mai taken Sarkin Samarin Dakwa, Ubangiji Allah ya kai kowa gidansa lafiya, mun gode mun gode Allah ya saka wa kowa da alheri.
Hakika lallai matasa sun ba da gudunmawa sosai, kuma in sha Allahu za mu tsaya kai da fata mu ga duk abubuwan da basu fi karfimmu ba za mu iya tsayawa tsayin daka mu ga mun kare wa matasa hakkinsu, mun gode, mun gode Allah ya saka da alheri. Hakazalika ya yi kira ga matasa da su guji shaye-shaye, domin shaye-shaye ba su da amfani a rayuwa.
” Sannan kuma muma za mu ba da gudunmawar daidai gwargwado domin duk wand aka ji ya lalace to akwai wadanda suka lalata shi, in sha Allahu idan akwai na sama da shi in suka tsawatar masa to zai kokari ya ga daina domin ya ga ya girmama su,”in ji shi.
Bugu da kari ya ja kunnen matasa a duk fadin kasar nan da su ni sanci ‘yan siyasar da za su yi amfani da su wajen basu kayan maye domin su yi bangar siyasa idan zabe ya zo.