Jama’a barkanku da kasancewa tare da Shafin Taskira, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da matsalar da ke addabar al’umma ta fannin kananan yara. A lokutan baya kadan, matsalar fyade (Lalata kannanan yara) na yawaita ne ga kananan yara Mata ko kuma manya, sai dai a yanzu wannan matsalar ta zama ruwan dare gama duniya, Yayin da take zagawa da kara yawaita ga kananan yara maza har ma da manya, ta yadda ake samun wasu gurbatattun mutane, kama daga matasa, manya Maza da sauransu, ke kokarin ganin sun yi amfani da kananan yara Maza, wanda kuma hakan ke illatar da kananan yaran, da jefa su cikin mawuyacin hali, ta hanyoyi daban-daban.
Ko me yake janyo yi wa yara kananan Maza fyade?,
Wanne matsaloli hakan ke iya haifarwa?, ko laifin wane ne tsakanin iyayen?, ta wacce hanya za a bi domin magance wannan matsalar?, Wacce shawara za a bawa iyayen yara?. Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikjn mabiyansa inda suka bayyana nasu ra’ayoyin kamar haka:
Sunana Hadiza D. Auta Kaura Jihar Zamfara:
Hakikanin gaskiya wannan badala ce mai zaman kanta, fyade ko ga ‘ya’ya mata babban hadari ne a rayuwa, balle ga ‘ya’ya maza da ba su da muhallin hakan matukar ba an yi ci da karfi ba. Abin da ke janyo matsalar kuma rashin dabi’a mai kyau ga wasu manyanmu, wadanda suke danne hakkin yara matasa da kananu, domin biyan bukatar kansu. Yala’alla don samun dukiya, mulki, ko kuma wata daukaka abin tinkaho.
wanda abu ne a bude ko a can baya zamanin Annabi Ludu Ubangiji ya la’anci mai yin wannan mummunar dabi’a. Sannan kuma an yi umurnin kashe wanda ya yi da wanda aka yi wa cikin gaggawa, saboda gudun yaduwar badalar a tsakanin al’umma.
Babbar matsalar da hakan yake haifarwa akwai manyan cutuka da ke karya garkuwar jiki, cikinsu kuma akwai; ciwon kanjamau, sanyi, dubura da rashin natsuwar zuciya. Kuma hanya daya ce da za a bi domin a magance ta a duniya, ita ce a bi dokar Allah kamar yadda aka yi umurni a kashe wanda ya yi da wanda aka yi wa gaba daya, kuma nan take. Sannan shawara ga Iyayen yara a koyaushe su kula da amanar da Allah ya ba su wurin kula da tarbiyyar ‘ya’yansu, da sauke hakkinsu daidai gwargwadon karfinsu. Su ba su cikakkiyar kulawa a duk wani motsinsu, su ja su a jiki domin su san me suke so, mene ne ba su ra’ayi, ina suka je, sannan da wa suke hulda. Akwai yiyuwar idan aka bi wannan matakin a ci maganin wanzuwar matsalar sannu a hankali, Allah ya kara kare al’ummarmu gaba daya.
Sunana Princess Fatima Mazadu:
Allah ya kyauta kawai zan ce, dan in ka ce Allah wadarai! Toh ka karawa abun armashi ne, dan kullu yaumin ana so muna wa bayi masu aikata laifuffuka addu’a ko Allah zai sa su dace. Amma abun yayi yawa a al’umma, son zuciya da son duniya zai sa suna sabawa Allah dan samun wata bukata ta su. Sai ka ga dan raini da raina addini ma a masallaci ake aikata badala, abun takaici abin bakin ciki, dan da ka haifa ka zo kana hakewa kaico, Neman duniyar dai kamar yadda na fada, da biyewa rudin shaidanu ko na ce rudin zuciya.
Abin da ke janyosu son duniya ne da ake rudarsu da shi, wasu arziki wasu kuma sha’awar yaran ke zuciyarsu. Ba zan ce karancin addini ba, sai dai na ce zallar zalunci ke janyo hakan, Laifin zuciya. Yanke hukunci ta yadda Allahu subhanahu wata’ala ya fadi da yadda manzon Allah (SAW) ya kwatanta ya kuma ba da umurnin yadda za a hukuntasu, shi zai sa a rage in har ana hukunta su, kamar yadda shari’a ta tanadar abun zai lafa, Killace yaran, Kulawa da su, Tarbiyya da yawan tunatar musu da tsoron Allah da tsoron aikata alfahsha, Rage saka musu fina-finan batsa, Rage yawan aiken yara lunguna magriba ko asubahin fari, Tsoratasu da yawo in ba su sanar da iyayen na su ba.
Sunana Amina Jibril Slimzy daga Jihar Kaduna:
Toh! abin da zan ce game da fyade da ake yi wa yara maza sai dai innalillahi wa innah ilaihi rajiun, kawai tabarbarewa da lalacewar rayuwa ce kawai hade da zamani. Abin da yake jawo hakan shi ne; yawanci sha’awa ce da son zuciya. Matsalar da hakan ke jawowa shi ne; wani sanadin fyaden nan da akai masa zai haifar masa da rashin lafiya rashin rike ba haya, sanan laifin iyaye ne da kuma hukuma na rashin daukar mataki kwakkwara akan dik wanda aka kama da hakan. Hanyar da za a bi don magance wanan matsalar ita ce; ta hanyar daukar mataki akan duk wanda aka kama da wanan laifin, idan ana daukar mataki da horo mai tsanani ga masu yi za a samu sauki sosai. Shawara iyaye su sa ido sosai akan yaransu, da tarbiyyarsu da irin mutanen da suke mu’amalar rayuwar yau da kullum, da gargadinsu akan karbar abun hannun mutane dan wani yaron da abun duniya ake ruddarsa a cuci rayuwarsa Allah ya kare mu ya kare mana zuri’a.
Sunana Masa’ud Saleh Dokadawa:
A gaskiya yin fyade ga kananan yara Maza, har ma da matan mu kanana. Musiba ce wacce za ta iya janyo dukkan musifu da bala’o’i a bayan kasa. Sannan rushewar mutunci da kima da darajar wanda aka yi wa ne, musamman ma yara mata, yin luwadi yana kawo faruwar cututtuka da suke bawa maza illa har karshen rayuwarsu ko da sau daya aka taba yi da su. Abin da ke janyo fyade ga yara Maza akwai sakacin iyaye, barin kango da yawa a cikin unguwa, rashin sanya idanu akan mutanen da ba a san halinsu ba, karancin tsoron Allah da saurin kwadayi ga yaran.
Matsalolin da yake haifarwa akwai Rashin lafiyar dubura, fitar musu da jini, illata jijiyar baya, ci gaba da yin abin idan ya ratsa duburarsu. Laifin iyaye ne, da al’umar da ake bawa amanar yara kamar malaman makarantu, sakacin mahukunta in an kama mutumn da laifin. Hanyoyin magance matsalar sun hada da sa’idon iyaye akan ‘Ya’yansu, tsoratar da su akan nuna rashin yadda da mutanen da ba a yadda da su ba, rage yawan jangwaye, ko wasu wurare masu duhu, tabbatar da zuwan yara inda suka tafi kamar makaranta ko aike, sai kuma daukar mummunan hukuncin shari’a akan wanda ya aikata laifin. Su ji tsoron Allah wajen kula da amanar ‘ya’yansu da Allah, ya dora masu, gargadin malamai, nasiha, jan hankalin yara akan yadda za su guji bin mutane wani wuri na daban, haduwar commette unguwa dan sa’idon zirga-zirgar yayansu.
Abba Fage:
Abin da yake sawa ana yi wa yara maza fyade shi ne; Akwai dalilai, Misali; Asiri ko tsafi, Neman duniya, Rashin aure ga su manyan maza din, a takaice kenan. Abin da ke janyo hakan shi ne; Rashin kulawa ga yaran ina za su je?, daga ina suke?, da rashin zama da su maza wajen jin meye damuwarsu saboda a magance musu. Hanyar magance wa fadakarwa da jan hankali da hukunci mai yawa ga wanda aka kama ya aikata hakan da rage wahalar aure. Iyayen yara shi ne; suna lura akan ina ne ‘Ya’yansu suke zuwa da ba su abin da suke bukata saboda kar ma wani ya ja hankalinsu akan wancen hanyar.
Sunana A.Ibrahim daga Jihar Kano:
A gaskiya bai kamata sabida halaye ne ba na mutunan arziki ba, kuma duk mai irin wannan dabi’ar yin haka yana jawo fushin ubangiji, kuma akan haka ubangiji yana saukar da masifu iri-iri daban-daban, Allah ka ganar da masu yi su daina, muma da ba ma yi Allah ka kara shirya mana imaninmu. Abin da yake jawo haka rashin kulawa ta iyaye, abin da ya sa na ce haka, ya kamata ace iyaye a ‘society’ su kula da su wa suke mu’amala, kuma yin haka wannan dabi’a yana jawo fishin ubangiji da masifu, Allah kiyashe mu. Iyaye su sa ido wajan kula da ‘Ya’yansu haka ma jama’a su taimaka a hada karfi da karfe hukumomi wajan dakile wannan fitina.
Shawara ita ce; Iyaye su sa ido sosai wajan ina yaro zai je da wa-da wa yake yawo?, ta haka cikin hukuncin ubangiji za a sami gyara.