Kungiyar Dalibai ta Kasa (NANS), ta yi barazanar shiga zanga-zanga kan kara kudin makaranta ga dalibai da Jami’o’in kasar nan suka yi.
Mataimakin shugaban kungiyar, Kwamared Suleiman Sarki, ne ya shaida hakan a ranar Juma’a a Maiduguri lokacin da ya gana da ‘yan jarida.
- Sin Ta Yi Imani Da Karfin Jama’Ar Habasha Na Magance Harkokinsu Da Kansu
- Gidauniyar Abdulsamad Ta Bai Wa Hukumar NIS Kyautar 500m Don Inganta TsaroÂ
Sarki, ya ce, karuwar kudaden makarantar na cutar da dalibai sosai daga shiyyar Arewa Maso Gabas, wadanda suka sha fama da matsalolin ‘yan ta’adda na tsawon shekaru 13.
Ya ce, NANS ta bai wa Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) wa’adin mako guda da ta sauya matsayarta kan batun jarin kudin makarantar ko ta fuskanci zanga-zanga a fadin kasar nan.
Sarki, ya ce Jami’ar Maiduguri, ta kara kudin rajistar da kashi 200, inda ya nuna matukar damuwa kan karin kudin, inda ya misalta haka da cewa zai janyo matsaloli sosai ga dalibai.
Ya ce, “Kara kudin rajistar makaranta da wasu Jami’o’in Arewacin kasar nan suka yi, abun damuwa ne matuka gaya domin muddin dalibai suka kasa biyan kudin dole su fita daga makaranta, hakan kuma ba abin da zai janyo illa karuwar matasan da basu da abun yi a shiyyar Arewa Maso Gabas.”
Mataimakin shugaban, ya bukaci dalibai da kada su biya sabon kudin rajistar amma su jira matakin da NANS za ta dauka domin tuni suka fara tuntubar hukumomin gudanarwa na Jami’ar Maiduguri kan matakin.
Kana, ya kuma nemi masu ruwa da tsaki a fagen ilimi a fadin kasar nan da su fito su dakile shirin jami’o’in Gwamnatin Tarayya na kara kudin makaranta.
Hukumar gudanarwar Jami’ar Maiduguri a ranar 1 ga watan Disamban 2022, ta amince da sabon tsarin kudin rajistar, sakamakon karuwar kudaden koyo da koyarwa.