Akalla fasinjoji 31 ne akayi garkuwa da su a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari a tashar jirgin kasa a jihar Edo, kamar yadda wani jami’i ya bayyana.
Kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama’a na jihar Edo, Chris Nehikhare, a ranar Lahadi ya tabbatar da cewa an yi garkuwa da fasinjoji 31 da ke shirin tafiya a harin da aka kai a tashar jirgin kasa ta Igueben.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa fasinjojin suna jiran jirgin karfe 4 na yamma wanda zai tashi daga tashar Igueben zuwa Warri ne a lokacin da ‘yan ta’addan suka kai harin, inda suka yi ta harbe-harbe, suka yi awon gaba da fasinjoji tare da jikkata wasu da dama.
Kwamishina Mista Nehikhare, ya shaida wa manema labarai a Benin cewa fasinja daya da aka sace ya tsere daga hannun masu garkuwar sannan kuma jami’an ‘yansanda sun yi nasarar kama daya daga cikin wadanda ake zargin.
Ya ce harin shi ne “mafi muni” da ya faru a jihar Edo a wannan lokutan.