Iyalan ‘yansanda 20 da suka rasa rayukansu a Jihar Anambra sun karbi diyyar Naira miliyan 43.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar Anambra, Mista Echeng Echeng ne, ya mika musu kudin a ranar Talata a hedikwatar rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra.
- Shugaban DSS Ya Magantu Kan Rikicin Matarsa Da Abba Gida-Gida Da Ya Barke A Kano
- ‘Yansanda Sun Cafke Matar Da Take Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Bindigu A Jihar Zamfara
Leadership Hausa ta samu labarin cewa babban Sufeton-Janar din ‘yansandan ne ya umarci biyan tsarin inshorar iyalin don biyan kudin diyyar.
Yawan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai kan ofisoshin ‘yansanda da shingayen binciken ababen hawa ya janyo asarar rayukan ‘yan sandan da ba a taba ganin irinsa ba a jihar a ‘yan kwanakin nan.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga wanda ya bayyana cikakken bayani game da biyan diyyar, ya ce matakin wani shiri ne na Sufeto-Janar din ‘yan sandan Nijeriya, Usman Baba Alkali, domin kara kwarin gwiwar jami’an yaki da masu aikata laifuka.
Ikenga, ya ce wannan wani tsari ne na kyautatawa iyalan jami’an da suka mutu a bakin aiki tare da yabawa irin yadda suka sadaukar da rayuwarsu don inganta tsaro a kasar nan.